Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yankin Tigray: An kashe 'ƴan gudun hijira da dama - inji MDD
Shugaban hukumar da ke kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ya ce ya damu matuka da yadda ake kashe yan Eritrea da ke gudun hijira a Habasha.
A cewar Filippo Grandi matuƙar suka tabbatar da haka, to ko ba karamin laifi aka aikata ba ta fannin keta dokar ƙasa da ƙasa.
A kan haka ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya na bukatar cikakkiyar dama shiga sansanonin yan gudun hijira hudu da ke yankin Tigray.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce tursasa wa yan gudun hijira daga Eritrea zuwa wadannan sansanoni ba abu ne da za a lamunta ba.
Ana ci gaba da gwabzawa tsakanin rundunar sojin Habasha da yan kungiyar TPLF, a yaƙin da aka soma ranar 4 ga watan Nuwamba.
Gwamnatin shugaba Abiy Ahmed na iƙirarin ƙwace iko a yankin na Tigray kuma a cewarta yaƙi ya ƙare.
Amma shugabannin ƙungiyar TPLF sun ce har yanzu suna ci gaba da gwabzawa da dakarun gwamnatin Habasha.
Kusan yan gudun hijira 100,000 daga Eritrea ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a yankin na Tigray.
Kuma sun guje wa muzgunawa da tursasa musu shiga aikin soji ne shekaru da dama kafin barkewar rikicin da ake fama da shi a yanzu.