Matsalar Tsaro: Yadda 'yan bindiga 'suka kashe mutum 37 a wani kauyen jihar Zamfara'

Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Daruruwan mazauna yankunan karkara ne suka tsere daga muhallansu zuwa garin Kanoma da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara ta arewa masu yammacin Najeriya a makon da muke ciki.

Wannan na zuwa ne sakamakon hare-haren 'yan fashi na baya-bayan nan da suka tilasta musu yin gudun hijira.

Kauyuka sama da biyar ne wadannan hare-hare suka shafa wadanda suka hada da Dutsen Gari da Telli da Tsakuwar dan Abara da Fara Girke.

Maharan sun kona gidaje da dukiyar da har yanzu ba a san adadinta ba.

Wani mazaunin kauyen Dutsen Gari ya shaida wa BBC cewa fiye da mutum 30 aka kashe a kauyen nasu a ranar Litinin, sannan maharan suka afka wa sauran kauyukan ranar Talata.

"Bayan gwamnati ta ce an yi sulhu, ranar Lahadi yaranmu sun tafi daji aka kwace mashinansu aka kone.

"A ranar Litinin tun da asuba ko kari ba mu yi ba kawai suka afka wa karkararmu, abin da muka yi lissafi sun kashe mutum 37," in ji wani mazaunin Dutsen Gari.

Ya kara da cewa tun a safiyar da suka dirar wa kauyen suke abin da suka ga dama har karfe 1:00 na rana ba su tafi ba.

A cewarsa "Babu ko jami'in tsaro daya da ya kai mana dauki tsawon wannan loto da aka kwashe".

"Bayan sun watsike, sai ga su ranar Talata kuma, tun daga Santalli da Dutsen Gari da Tsakuwar dan Abara da Mahuta da Fara girke, duka wadannan garuruwan babu dukiya duk sun kone duk shagon da ke wajen sun bude sun kwashe dukiyar.

"Amma gwamnati da ta ga abin ya ki ci ya ki cinyewa ta aika jami'an tsaro a maraicen Talata mota shida zuwa Dutsen Gari," in ji shi.

Baya ga dukiyoyi wannan lamarin ya shafi mata da kananan yara da ke rayuwa a wadannan yankunan.

Wata mata da ta nemi a boye sunanta ta shaida mana cewa, "a ranar Talata suka shiga suna can, da wuka suke yankar mutane, babu babba ba yaro.

Da aka tambaye ta ko ta ga wadanda aka yanka, sai ta ce: "Eh, na gani an yanki sama da 24 wadanda aka dauko, jiya an yanki bakwai, shi ya sa muka dawo garin Kanoma dan firgicin ya isa, kayanmu na can kuma wuta suke ta kunna wa gidajen mutane duk sun kone abinci.

"Yaranmu da dama na can ba mu san inda suke ba duk sun halaka, ba a batun dabbobinmu, ban san inda mijina yake ba, yarana 10 biyu ne kawai a hannuna, da na goye da yayansa," in ji wata mata.

Ta kara da cewa ba ta san inda sauran yaranta takwas suke ba ya zuwa yanzu.

Wata mata da ta kwashe kwana hudu a garin na Kanoma ta ce ita ma ba ta tare da mijinta kuma ba ta san inda duka yaranta suke ba, domin kuwa kowa takan shi yake.

Abubakar Muhammad Dauran, kwamishinan tsaro na jihar, ya ce sun samu labarin wadannan hare-hare, kuma sun tura jami'an tsaro wurin da abin ya faru.

Sai dai ya ce ai san adadin mutanen da suka rasu ba.

A cewarsa: "Gaskiya ba ni da sahihin adadin mutanen da suka mutu; ina dai jiran jami'an tsaro su ba mu rahoton takamaiman wadanda aka kashe".

Wadannan hare-hare na zuwa ne a yayin da jami'an tsatron kasar suke cewa suna samun galaba a kan masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Jihari Zamfara na daga cikin jihohin arewa maso yamma da ke fama da tashe-tahsen hankula sakamakon hare-haren 'yan fashin daji.

Amma hukumomi sun ce ana samun sauki na hare-haren, kodayake mazauna yankunan sun musanta hakan.