An gurfanar da iyaye a Kaduna saboda 'wulaƙanta haƙƙin ƙananan yara'

Bayanan sautiHirar Mukhtari Adamu Bawa da Kwamishiniyar walwalar jama'a a Kaduna
An wallafa

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta gurfanar da iyayen wasu yara 22 a gaban kotu, bisa tuhumar fataucin ɗan'adam da wulaƙanta haƙƙin ƙananan yara.

Ta ce sojoji da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da fataucin bil'adama ta Nijeriya (NAPTIP) ne suka kuɓutar da yaran lokacin da ake safararsu zuwa jihar Nasarawa don yin aikin ƙwadago.

Hukumar NAPTIP ta ce yanayin da ake safararsu cunkushe a mota ƙirar J5, babu ko kafar shan iska ne ya ja hankalin jami'an tsaro da suka kama direban, tare da kuɓutar da yaran waɗanda suka fito daga ƙaramar hukumar Soba.

Hafsat Muhammed Baba, kwamishiniyar walwalar jama'a a jihar Kaduna, ta shaida wa BBC cewa yaran a yanzu suna cikin ƙoshin lafiya kuma ana kula da su.

Ta nuna takaici kan ɗabi'ar wasu iyaye na ɗora wa yaransu alhakin ciyar da su wanda matsala ce da ta ce ake fama da ita a Arewacin ƙasar.

A cewarta, gwamnati za ta ci gaba da bibiyar batun domin ganin hukuncin da za a yanke wa iyayen dai-dai da abin da dokar jihar ta kare martabar yara ta tanada.