Ruhollah Zam: Kasashen EU sun kauracewa Iran kan kisan dan jarida

Iran ta zargi dan jaridar da amfani da kafar sada zumunta wurin tada husuma.
Bayanan hoto, Iran ta zargi dan jaridar da amfani da kafar sada zumunta wurin tada husuma.
An wallafa

Hudu daga cikin manyan kasashe masu fada aji a Tarayyar Turai sun fasa halartar taron kasuwanci da Iran ta gayyace su a Tehran, bayan da ta zartar da hukuncin kisa kan dan jaridannan Ruhollah Zam.

Jekadun kasashen Faransa da Jamus da Italiya da Austria sun sanar da matakin janyewa daga halartar taron da aka tsara yi ta internet yau Litinin a birnin Tehran.

Jim kadan bayan samun labarin ficewar kasashen ne Iran ta sanar da cewa za ta dage taron zuwa wani lokaci.

Kisan Ruhollah Zam ya haifar da tsamin dangantaka tsakanin Iran da kasashen Turai kan abinda suka kira rashin imani da ba za su lamunta ba.

Iran ta zargi dan jaridar da amfani da kafar sada zumunta wurin tada husuma.

Kuma a shekarar 2017 ne ya samu mafaka a Faransa bayan wallafa zanga zangar kin jinin gwamnati a shafukansa na sada zumunta.

Daga baya sojojin Iran suka cafke shi a Iraƙi suka maida shi gida, inda kuma aka rataye shi a ranar Asabar.

Matakin kasashen ya fusata Iran, kuma yanzu haka ta gayyaci jakadun kasashen Faransa da Jamus don tattauna batun.

Itama kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi tir da kisan Ruhollah Zam.

Kuma ta ce hukumomi sun yanke masa hukuncin kisa ne bayan sun tursasa masa amsa laifin da bai aikata ba.