Kasafin kuɗin 2020: Galibin ƴan Najeriya ba su gani a ƙasa ba - Ƙungiyar farar hula

Buhari ya gabatar wa majalisa kasafin naira tiriliyan 13.08 na shekarar 2021.

Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

An wallafa

Masu sa-ido a kan harkokin shugabanci a Najeriya sun fara ƙalubalantar ikirarin da shugaban ƙasar ya yi cewa gwamnatinsa ta yi nisa wajen aiwatar da kasafin kudin wannan shekarar ta 2020.

An yi ƙiyasin kasafin kuɗin na bana zai ci naira tiriliyan 10, duk da cewa an sake rage shi bayan ɓullar annobar cutar korona.

A lokacin da yake gabatar da kasafin kudin, Shugaba Buhari ya ce gwamnati ta damƙa wa ma'aikatu da hukumominta a ƙalla kashi 50 cikin 100 na kasafin kuɗin da aka keɓe musu a shekara mai ƙarewa.

Amma wasu ƙungiyoyi da ke sa ido a kan gwamnati na ganin cewa ikirarin ya saɓa da ayyukan da gwamnati ke yi a zahiri.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa tafiya ta yi nisa wajen aiwatar da kasafin kudin, kuma gwamnati ta aiwatar da manyan ayyuka a ɓangarorin rayuwa daban-daban, ciki har da noma da samar da wutar lantarki, da gina hanyoyi da sauransu.

To sai dai Comrade Kabiru Dakata na ƙungiyar da ke bibiyar yadda gwamnatoci a matakan tarayya da jiha ke gudanar da kasafin kuɗaɗensu wato KAJA, ya ce abin da shugaban ya faɗa ya yi hannun riga da abin da ke zahiri.

Ya ce ''alƙaluman da ke fitowa daga hukumomi daban-daban sun nuna cewa ayyuka yi sun ragu, kuma kullum sai ƙara samun talakawa ake yi.''

Ya ƙara da cewa ''a kasafin kuɗin na shekarar 2020 an gaza sosai domin ba a samun alƙaluman su yi daidai da abubuwan da ake gani a zahiri.''

Kungiyoyin da ke sa`ido a kan gwamnati na ganin cewa ikirarin ya saba da ayyukan da gwamnati ke yi a zahiri.

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Batun aiwatar da kasafin kudi dai na cikin ƙalubalen da mahukunta ke fuskanta, inda sau da yawa gwamnatoci ba sa iya aiwatar da abin a zo a gani a cikin kasafin kuɗinsu na shekara-shekara.

Duk da cewa mahukunta kan kafa hujja da wasu alƙaluma, wasu 'yan Najeriyar na cewa alƙaluman da ake rubutawa a kan takarda sukan ci karo da aikin da aka aiwatar a zahiri.