Sau nawa Ganduje ya yi wa dokar Masarautun Kano kwaskwarima?

..
    • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
  • An wallafa

Matakin da majalisar Dokokin jihar Kano da ke Najeriya - wacce ake kallo a matsayin 'yar amshin shatar Gwamna Abdullahi Ganduje - ta ɗauka na amincewa da dokar naɗa Sarkin Kano a matsayin shugaban dindindin na Majalisar Sarakunan jihar ya bijiro da tambaya kan adadin gyaran fuskar da gwamnati ta yi wa dokokin Masarautar a 'yan shekarun nan.

Kamar yadda ya faru a baya, gwamnatin jihar ce ta buƙaci majalisar ta yi wa dokar kwaskwarima.

Gabanin sauya wannan doka, dokar masarautu ta jihar ta ce za a riƙa yin karɓa-karɓa a shugabancin majalisar sarakuna jihar guda biyar duk bayan shekara huɗu.

Takun saƙa ko kuma zaman doya da manjan da ake zargin an yi tsakanin tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II da kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sa gwamnan yi wa dokar Masarautun jihar kwaskwarima lokaci zuwa lokaci.

Sa-toka-sa-katsin da ke tsakanin gwamnan da tsohon sarkin ta samo asali ne sakamakon sukar da sarkin ya rinƙa yi wa wasu manufofi ko kuma ayyuka na gwamnan Kano. Duk da cewa babu wata cikakkiyar hujja a bayyane, an zargi tsohon sarkin da ƙin goyon bayan Ganduje a zaɓen 2019 inda har wasu ke zargin cewa tsohon sarkin ya goyi bayan ɗan takarar PDP Abba Kabir Yusuf.

Tun bayan zaɓen 2019, jama'a da dama suka fara zargin cewa gwamnan Kano zai tuɓe Sarki Sanusi daga sarautar Kano, sai dai hakan bai faru nan take ba, wanda kwatsam sai gwamnan ya aika wa majalisar da buƙatar ƙarin masarautu a jihar domin su zama biyar.

A ranar Laraba, 15 ga watan Mayun 2019 ne gwamnan jihar ya rattaɓa hannu a kan sabuwar dokar kafa sabbin masarautun bayan majalisa ta amince da kudirin gwamnan.

Sabbin masarautun sun haɗa da Rano da Bichi da Gaya da Ƙaraye, sai kuma shi Muhammadu Sanusi II a lokacin aka mayar da shi Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.

Sarakunan da aka naɗa sun haɗa da Alhaji Aminu Ado Bayero wanda aka ba jagorancin masarautar Bichi, da kuma Dakta Ibrahim Abubakar a matsayin sarkin Ƙaraye sai Tafida Abubakar Ila a matsayin Sarkin Rano da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya.

Rushe sabbin masarautun Kano

..

Asalin hoton, TWITTER/@DAWISU

Masu lura da lamura sun ce wani dalili da ya sa gwamnan Kano ya sake yin kwaskwarima ga dokar Masaratun Kano shi ne wani hukuncin da kotu ta ɗauka a jihar na rushe sabbin masarautun da Ganduje ya kafa a watan Mayun 2019.

Kotun dai ta ce gwamnatin ta Kano ba ta kafa masarautun kan ƙa'ida ba. Wannan ne ya sa gwamnan ya sake aika wa Majalisar Kano da wani sabon kudiri na kafa sabbin masarautu huɗu a jihar.

Ba da daɗewa ba majalisa ta yi karatu na farko da na biyu har ta amince kuma ta tura wa Gwamna Ganduje ya sake saka hannu domin tabbatar da su a matsayin masarautu masu iko kuma da martaba ta ɗaya a jihar.

Matakin majalisar na amincewa da kudirin a wannan karon ya zo ne duk da umarnin wata babbar kotun jihar na cewa kada wanda ya ɗauki wani mataki kan batun har sai ta saurari ƙarar da masu zaɓar sarkin Kano suka shigar gabanta, suna kalubalantar ƙirƙiro sabbin masarautu a jihar.

Tanadin da dokar ta yi

  • Gwamna ne zai zaɓi shugaban majalisar sarakuna
  • Gwamna ne zai naɗa masu zaɓar sarki a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso
  • Duk sarkin da gwamna ya zaɓa don shugabantar majalisar sarakuna, zai jagoran ce ta ne tsawon shekaru biyu
  • Duk sarkin da yaƙi halartar tarukan majalisar sarakunan har sau uku ba tare da kwakkwaran dalili ba, ya kori kansa daga sarauta.
..

Sabuwar kwaskwarima

A watan Yulin bana ne Sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya bai wa Aminu Babba Ɗan Agundi sarautar Sarkin Dawaki Babba, kusan shekaru 17 kenan bayan marigayi Ado Bayero ya sauke Ɗan Agundin daga sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta.

Kwanaki kaɗan bayan bayar da wannan sarauta ne Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya buƙaci Majalisar Kano ta sake yi wa dokar masarautun jihar kwaskwarima domin saka Sarkin Dawaki Babba a cikin masu zaɓen sarki.

A baya dai masu zaɓen sarkin su ne:

  • Madakin Kano
  • Makaman Kano
  • Sarkin Dawaki Mai Tuta
  • Sarkin Bai

To sai dai a ranar 8 ga watan Satumbar 2020 Majalisar Jihar Kano ta amince da buƙatar da gwamnan ya kai a gabanta tun a baya, inda ta amince da saka Sarkin Dawaki Babba a matsayin masu zaɓar sarki, a halin yanzu, da zarar gwamnan jihar ya saka wa dokar hannu masu zaɓen sarki a Masarautar Kano za su zama biyar saɓanin huɗu da ake da su.

Shugaban Sarakunan Kano na dindindin

...

Asalin hoton, AMINU ADO BAYERO/INSTAGRAM

A cikin gyaran da aka yi wa dokar Masarautun Kano ta 2019, cikin tanade-tanaden har da batun cewa gwamna ne zai zaɓi shugaban majalisar sarakuna kuma duk sarkin da gwamna ya zaɓa don shugabantar majalisar sarakuna, zai jagoran ce ta ne tsawon shekaru biyu.

Sai dai daga baya gwamnatin jihar ta sake shawara bisa hakan bayan da Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Kano bayan da aka tuɓe Muhammadu Sanusi II a watan Maris.

Gwamnatin jihar ta buƙaci Aminu Ado Bayero ya zama shugaban majalisar sarakunan jihar na dindindin inda a ranar 8 ga watan Satumba ne majalisar jihar ta amince da hakan.

Gwamnatin jihar ta sauya dokar a maimakon tsarin na karɓa-karɓa tsakanin manyan sarakunan jihar guda biyar.

Karin labarai da za ku so ku karanta: