Matar da ke sayen iskar da take shaƙa kullum ta N5,000 a Najeriya
Da wuya ka samu wadanda za su gasgata ka idan ka fadi cewa wani dan adam na sayen iskar da yake shaƙa.
To BBC ta tattauna da wata baiwar Allah ƴar Najeriya, wadda ba za mu ambaci sunanta ko kuma bayyana hotonta ba domin kare mutuncinta, wadda kuma take sayen iskar Oxygen a kullum ta naira fiye da 5000.
Allah Sarki! Cikin yanayin karkarwar murya da zubar da hawaye wannan baiwar Allah ta ce "ko ina da sauran rabon fita na wataya kamar yadda sauran jama'a ke yi. Allah ka ba ni ikon cin wannan jarrabawar da ka ɗora min."
Da ka shiga dakin wannan baiwar Allah abin da idanunka za su fara gane maka shi ne yadda jikinta ya yi baƙi-ƙirin amma fuskartar da haskenta.
Baya ga wannan kuma abin da kunnuwanka za su fara jiye maka shi ne ƙarar fitar iskar gas daga cikin wasu manya-manyan tukwane da ke harba iskar Oxygen zuwa hancinta ta hanyar wasu siraran bututai.
"Da wannan nake numfashi saboda na taɓa samun daukewar numfashi cikin dare inda aka kai ni asibiti kuma likitoci suka ce dole sai na saya idan dai har ina son na rayu.
Na sayi daya 650,000 amma yana wurin gyara, to kuma wannan wanda shi ne na biyu na saye shi 350,000. Sannan ga wannan wanda ba ya amfani da wuta inda na sayi tukunyar gas din naira 65,000 sannan a rinka zuba Oxygen din naira 15,000."
"Likitoci sun kuma ce min sai na sayi na goyawa a baya saboda fita daga gida wanda kudinsa ya fi naira 200,000", in ji mai shaƙar iskar Oxygen.
Ta kuma kara da cewa "likitoci hudu nake gani inda kowanne ke rubuta maganin da za a saya ban da kudin ganin likita. Kafin annobar korona, ina kashe kudi fiye da naira dubu 70 a kowane wata."
Wace cuta ce ke damun ki?
"To cuta ce dai ta numfashi da likitoci ke kira Pulminary hypertention, cuta ce wadda ta taba min zuciya da huhuna wato jini ba ya kai wa ga zuciya yadda ya kamata.
Na kai shekara uku da fara wannan cutar. Fatata ce ta fara yin baki sannan daga bisani bayan yin gwaje-gwaje aka gano cewa akwai wannan cutar.
Sun ce garkuwar jikina na da karfi inda suke fada da junansu maimakon su ba ni kariya sai suka taba zuciya da huhu.
Tun kafin ma likitoci su fada min cutar da ke damu na ni ina jin rashin dadi a jikina."

"Ban san dalilin da ya sa mai gidana ya sake ni ba"
Da aka tambayi wannan baiwar Allah ko ina mai gidanta yake? Sai ta ce:
"Muna zaune lafiya lau sai kawai ya nemi mu rabu. Na ta ba shi hakuri kan cewa don Allah ka da ya sake ni. ''Babu abin da na yi masa. Ko musu ba na yi masa. Babu irin biyayyar da ba na yi masa.
''Amm duk da haka wata rana sai ya aiko min sakon waya cewa ya sauwake min Allah ya hada kowa da rabonsa. A lokacin ma ina kwance domin samun saukin bai kai na yanzu ba.
Yarana guda biyar, hudu na mijina na farko inda daya kuma na mijin da muka rabu.
Da haka nake dawainiya da su ta makaranta da abinci. Sannan kuma ga kudin haya wanda zan biya a wannan watan domin mai gidan har ya turo yana neman kudi amma ba ni da su."

"Babu wanda ke tallafa min kan wannan cutar sai dangina"
"Ni ban taba zuwa neman taimako wurin wani ko gwamnati ba saboda sai na ji kamar na wulakanta kaina ko kuma na yi wa Allah butulci.
Ni gaskiya ma ban san wurin wanda zan je na nemi taimako ba duk da ina bukatar hakan.
A irin wannan yanayin ne mutum ke gane mai ƙaunarsa"
Akwai yiwuwar zan warke
"E wasu likitoci sun ce min zan iya warkewa daga wannan cutar kamar yadda marasa lafiya da dama kan warke.
To sai dai wasu likitocin guda biyu sun ce min ba a warkewa sai dai ka yi ta shan magani har karshen rayuwa kamar yadda masu hawan jini da cutar suga suke yi.
Sai dai sun gargade ni ka da na bari magani ya yanke min ko kuma ita iskar Oxygen din da nake shaka.
Na kan yawan yin tunanin ko wata rana zan warke.
To amma idan na tuna akwai wadanda suna can ruwa ma sai an diga musu sai na yi wa Allah godiya na roke shi domin samun damar cin wannan jarrabawa."
Komai a wahalce

Asalin hoton, Others
Wannan ciwo ya sa wannan mata komai za ta yi a wahalce take yin sa. ''Ko daga nan zuwa ban ɗaki zan shiga sai na dinga numfarfashi, balle kuma a ce zan fita dn zuwa asbiti.
''To kafin na kai bakin get din gidana ma na gama jigata. Rayuwar dai sai godiyar Allah kawai,'' in ji ta.
Ta ci gaba da cewa: ''Ana so a kullum na riƙa shan iskar oxygen ta sa'a 16 zuwa 19. Lallai wannan kaɗai ya ishi ɗan adam tsoron Allah. Iskar da ake gani kamar ba ta da muhimminaci ni ga shi sai na saye ta nake samu na shaƙa.''
Baya ga sayen iska matar ta kuma ce a ƙalla tana shan maganunguna kala biyar a kowace rana, cikinsu akwai wanda duk na rana ɗaya ya kan kai naira 4,000.











