'Yan fim sun yi wa hukumomin Sudan rubdugu saboda kama 'yan uwansu

Hajooj Kuka

Asalin hoton, Hajooj Kuka

Bayanan hoto, Hajooj Kuka
An wallafa

Kwararrun masana harkar fina-finai sun yi kira da a saki wasu 'yan fim biyar da hukumomi suka kama a Sudan, bayan da aka yanke musu hukuncin daurin wata biyu a gidan yari saboda haifar da fitina.

Daga cikinsu har da Hajooj Kuka, wanda aka yankewa hukunci ranar Alhamis, tare da wasu abokan aikin sa guda hudu dukkanninsu 'yan kungiyar "Civic Lab" bayan samunsu da laifin da ake zargin sun aikata.

An kirkiro kungiyar ne bayan zanga-zangar da aka yi a shekarar da ta gabata wacce ta janyo hambarar da shugaba Omar al-Bashir daga shugabancin kasar.

Wani mai shirya fim Steven Markowitz, wanda ya shirya fim din da Kuka ya dauki nauyi a kwanan nan mai suna "aKasha" da aka haska a bikin baje kolin fina-finai na Venice, ya yi Alla-wadai da abin da ya kira "zarge-zargen karya''

Shima Markowitz Cameron Bailey, daraktan bikin baje kolin fina-finai na kasa da kasa na Toronto, ya ce "Hajooj Kuka fitaccen mai shirya fina-finai ne, don haka kamata ya yi ayi ta yamadidi da al'amarin har sai hukumomi sun sake shi tare da sauran wadanda aka kama.

Fastar fim din Beats of the Antonov

Asalin hoton, @HajoojKuka

Bayanan hoto, Fastar fim din Beats of the Antonov

Wani fim din Kuka mai suna "Beats of the Antonov", ya lashe lambar yabo ta Toronto da aka yi a shekarar 2014, kuma ba da jimawa ba aka gayyaci mashiryin fina-finan zuwa babbar Kwalejin Koyar da nadar hotunan bidiyo ta Sudan.

Fim din na kunshe da kade-kade da raye-rayen mutanen wani yankin Sudan da ake kira Nuba, da aka mayar saniyar ware wanda kuma gwamnatin tsohon shugaba Al-Bashir ta sha yin ruwan bama-bamai a cikinsa a yakin basasar kasar da aka yi daga shekarar 1983 zuwa 2005.

Wani lauya Othman al-Basri ya ce wata kotu da ke birnin Khartoum ce ta yanke wa Kuka da sauran masu shirya fina-finan su hudu hukuncin daurin watanni biyu a kurkuku da tarar fan dubu biyar na Sudan.