Magajin Gari da ke son korar motoci daga birninsa

An wallafa

Magajin Garin Pristina babban birnin kasar Kosovo ya bayyana wani shiri na zaftare yawan ababen hawa da ke shiga birnin saboda yace motoci na neman 'hallaka' birnin.

Mista Shpend Ahmeti ya ce tun da aka kullace mutane a gida saboda cutar korona, kuma motoci suka bace daga titunan birnin - an sami raguwar cunkoso da bunkasar muhalli a birnin.

Magajin Garin ya sha alwashin rage yawan ababen hawan da zarar annobar korona ta shude, kuma ya ce Prishtina kyakkyawan birni ne da bai kamata a bari motoci su lalata ba.

Magajin Garin, Shpend Ahmeti ya bayyana aniyarsa ta daukan mataki kan matsalar da cunkoson ababben hawa kan janyo wa birnin Pristina - birnin da ya ce motocin hawa na neman hallaka wa saboda yawansu.

A wani sakon Twitter da ya wallafa, Magajin Garin ya ce da zarar an ga bayan annobar korona a kasar Kosovo, gwamnatin da yake jagoranta za ta fitar da wasu sababbin matakan da za su rage yawan ababen hawa a cikin birnin - ciki har da wani sabon haraji da za a fara karba daga duk wanda ya ke son shiga kwaryar birnin da motarsa.

Akwai kuma caji na musamman idan mutum na son ajiye motarsa a bisa titunan birnin bayan hana motoci bin wasu hanyoyin baki daya.

Tun bayan da annobar korona ta bayyana, manyan biranen duniya masu yawa sun sami ingantacciyar rayuwa ta irin iska mai kyau da mutane kan shaka da raguwar hayakin mota mai gurbata muhalli da kuma natsuwar da ke wanzuwa saboda rashin rugugin ababen hawa.

Ana iya cewa ke nan ta wannan fannin, annobar ta taimaka wajen bunkasa yanayi, kuma manyan birane za su so daukan matakai irin na birnin Pristina.