Gwamnatin Legas ta samar da cibiyar killace masu coronavirus mai gadaje 110

Legas

Asalin hoton, Twitter/@jidesanwoolu

An wallafa

Jihar Legas da ke kudancin Najeriya inda cutar numfashi ta coronavirus ta fi kamari a kasar ta sanar da matakinta na samar da wata cibiyar killace masu fama da cutar.

Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar da haka a shafin Twitter inda ya ce gwamnatinsa ta yi hadin gwiwa ne da bankin GT, daya daga cikin bankunan da ke gudanar da harkokinsa a kasar wajen samar da cibiyar.

A cewarsa, cibiyar na da karfin daukar marasa lafiya 110 musamman wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ta covid-19.

A jihar ta Legas, mutum 59 ne suka kamu da coronavirus cikin mutum 97 da ke dauke da cutar a Najeriya.

Gwamnan ya sake jaddada kudirinsa na ganin an yaki coronavirus a jihar tare da rage bazuwarta musamman daga mutanen da suka dawo daga kasashen waje.

Kazalika, Ma'aikatar Lafiya a Legas din ta yi hasashen cewa mutum 39,000 ka iya kamuwa da cutar a jihar.

Sai dai gwamnatin jihar na ci gaba da daukar matakai daban-daban na hana bazuwar cutar ciki har da umartar mutane su zauna a gida tare da nesa-nesa da juna.

Gwamnatin ta kuma dauki matakin yin feshin magani domin kashe kwayar cutar ta covid-19.

Covid-19

Asalin hoton, Twitter/@jidesanwoolu

Bayanan hoto, Sabuwar cibiyar kebe masu fama da coronavirus a Legas

Haka ma hukumar dakile yaduwar cutuka a Najeriya NCDC ta ce mutumin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka Aliko Dangote ya bai wa Legas gudummawar motocin daukar marasa lafiya har hudu domin tallafa musu a kokarin da ake na dakile bazuwar cutar a Najeriya musamman a jihar ta Legas.

Covid-19

Asalin hoton, Twitter/NCDC

Bayanan hoto, Motocin da attajirin Afirka Aliko Dangote ya bai wa gwamnatin Legas domin yaki da coronavirus