Coronavirus: Na yi gwaji ya nuna ba ni da cutar - Gwamnan Kebbi

Bagudu

Asalin hoton, Bagudu Facebook

An wallafa

Gwamnan jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya Abubakar Bagudu ya ce ya yi gwajin coronavirus saboda mu'amala da ya yi da wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar, sai dai sakamakon gwajinsa ya nuna ba ya dauke da ita.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Juma'a, sannan kuma ya ce babu bukatar yi wa jami'an gwamnatinsa gwajin tun da ba a same shi dauke da cutar ba.

Haka kuma a wani mataki na hana cutar shiga garin da dakile ta, gwamnan ya ce an dauki matakin takaita zirga-zirgar da ta hada da shiga da fita daga jihar saboda fargabar yaduwar coronavirus.

Ya kara da cewa dokar ba za ta shafi ma'aikatan gaggawa ba, irin su ma'aikatan lafiya da jami'an tsaro da masu kai magunguna da abinci da kuma gidajen sayar da man fetur.

Gwamna Bagudu ya kuma bayar da umarnin rufe dukkan makarantu ciki har da na Islamiyya da na allo sai abin da hali ya yi.

Ga cikakkiyar hirarsa da Halima Umar Saleh ku saurara ta hanyar latsa alamar lasifikar da ke kasa:

Bayanan sautiHira da Gwamna Abubakar Bagudu kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

A hannu guda kuma, gwamnan ya ce akwai fargaba kan yadda lamarin ke shafar tattalin arzikin kasashen duniya, sai dai duk da cewa bai fito karara ya ce ko hakan zai shafi biyan albashin jihar ba, ''ba fata ake ba, amma idan wannan annobar ta ci gaba to zai shafi kowa.''

Kan ko jihar ta shirya wajen tanadar kayayyakin da ake bukata a asibiti don tunkarar cutar, Gwamna Bagudu ya ce suna da na'urar da ke taimakawa wajen numfashi wato ventilato biyu, ''ba su wadatu ba, amma muna shirin saye sai kuma ga wannan abu ya zo.

''Sai dai masana harkar lafiya sun ce mana ventilato na da amfani amma ba a cika bukatarta a matakin farko na magance cutar ba sai an kai kurewa, wanda ba ma fatan hakan. Amma muna da wasu na'urorin na taimakawa wajen numfashi da yawa da za a iya amfani da su.''