Amurka da Taliban za su kulla yarjejeniyar zaman lafiya

Residents in the eastern city of Jalalabad celebrated the reduction in violence on Friday

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mazauna birnin Jalalabad a gabashin Afghanistan na murnar raguwar yaki a yankin
An wallafa

Ranar Asabar 29 ga watan Fabrairu ne ake kulla wata yarjejeniya mai cike da tarihi tsakanin Amurka da 'yan Taliban din kasar Afghanistan a birnin Doha.

Ana fatan yarjejeniyar za ta zama hanyar wanzar da zaman lafiya a kasar.

An shirya wannan yajejeniyar ne kan wani shirin janye sojojin Amurka daki-daki daga kasar inda a daya bangaren kuma 'yan Taliban za su tabbatar da sun mutunta tsagaita wutar da za akulla kana bangarorin kasar su samar da shirin zaman lafiya tsakaninsu.

Ministocin harkokin waje da jakadu daga kasashen fiye da goma ne za su halarci wannnan bikin, cii har da sakataren harkokin waje na Amurka Mike Pompeo.

An dai shafe fiye da shekara guda ana tattaunawa kan wannan yarjejeniyar a birnin Doha, ban da jerin tuntubar da aka rika yi a Kabul da wasu manyan biranen.

Wanan lokaci ne da ke cike da tarihi - kuma gagarumin yunkuri ne na kawo karshen yaki mafi dadewa da Amurka ta taba shiga - wanda kuma 'yan Afghanistan ke sa ran zai kawo karshen yakin da ya daidaita kasar na tsawon fiye da shekara 40.

Kwamandojin Taliban na ta aika wa mabiyansu cewa a karshe sun nasara a wannan yakin, kuma sun kayar da daular Amurka.

Amma yarjejeniyar za ta gwada karfin alkawarin da suka dauka na tabbatar da zaman lafiya da kuma hana Afghanistan sake zama wata matattara ga kungiyoyi masu ra'ayin rikau.

Ita kuma Amurka ta jingina janyewar da za ta yi kan cika wannan alkawarin da Taliban ta dauka.

Kuma idan suka cika alkawarin kamar yadda aka tsara, sojojin Amurka 5,000 cikin 13,000n da ke cikin kasar za su fara cikin watanni masu zuwa.

Donald Trump ya ce Taliban "na son kulla yarjejeniya"

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Donald Trump ya ce Taliban "na son kulla yarjejeniya"

Asarar rayuka a yakin Afghanistan

Su kuwa al'umar kasar Afghanistan - wadanda yaki ya raba da kwanciyar hankali - suna cike da fatan shirin zai yi nasara, amma kuma suna cikin taraddadi idan hakan bai samu ba.

Kusan sojoji 3,500 na kasashen waje ne suka rasa rayukansu a Afghanistan tun harin da aka kai can a 2001, cikinsu akwai Amurkawa 2,300.

Amma gano adadin fararen hula da 'yan tawaye da sojojin gwamnati Afghanistan da suka mutu zai yi wuya.

A wani rahoto da ya fito a Fabrairun 2019, Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da faraen hula 32,000 ne suka rasa rayukansu.

Wata cibiya da ke Jami'ar Brown University ta Amurka ta ce jami'an tsaro 58,000 da sauran mayakan da ke bangaren kungiyoyi masu adawa 42,000 ne suka halaka a sandiyyar rikicin.