Bisa 'kuskure' muka harbo jirgin Ukraine – Iran

Asalin hoton, Getty Images
Kasar Iran ta fito fili ta bayyana cewa bisa ''kuskure'' ne ta harbo jirgin Ukraine mai dauke da fasinjoji 176.
Shugaban kasar Hassan Rouhani ya bayyana cewa ajizanci ne irin na dan adam ya sa hakan ta faru.
A baya dai Iran ta yi watsi da hasashen da aka yi na cewa daya daga cikin makamai masu linzamin da ta harba ne ya kado jirgin a kusa da birnin Tehran a ranar Laraba.
Rundunar sojin Iran din ta bayyana cewa jirgin na Ukraine ya zo kusa da wani yanki da ke kusa da wani sansani na zaratan sojojin juyin-juya halin Iran wanda hakan ya sa suka yi zaton cewa daya daga cikin jiragen abokan gabar su ne, sai suka harbo shi.
An kakkabo jirgin ne dai jim kadan bayan jirgin ya tashi daga filin jirgin Tehran, sa'o'i kadan bayan Iran din ta harba makamai masu linzami ga sansanonin sojojin Iraki masu dauke da sojojin Amurka.
Shugaba Rouhani ya bayyana cewa wannan kuskure ne wanda ba za a yafe ba -- ya sha alwashin cewa masu hannu a wannan aika aikar za su fuskanci hukunci.
Jirgin saman dai na dauke da jimlar fasinjoji 176 a lokacin da ya yi hatsari inda 82 'yan kasar Iran ne.
Sauran 'yan kasashen sun hada da:
- 'Yan Canada 63
- 'Yan Ukraine 11, ciki har da ma'aikatan jirgin
- 'Yan kasar Sweden 10
- 'Yan Afghanistan hudu
- 'Yan kasar Jamus uku
- 'Yan Birtaniya uku











