Zakarun Turai: Chelsea ta tsallake rijiya da baya da cin Lille 2-1

Tammy Abraham da sauran 'yan Chelsea

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Tammy Abraham wanda ya fi kowa bajinta a wasan shi ne ya fara daga ragar Lille, da kwallon da ta kasance ta 13 da ya ci wa Chelsea a bana
An wallafa

Chelsea ta tsallake rijiya da baya, ta kai matakin gaba na kungiyoyi 16 a gasar Zakarun Turai, bayan da ta tsira a hannun Lille da ci 2-1, a Stamford Bridge.

Kungiyar ta kociya, Frank Lampard ta mamaye wasan a kusan gaba dayan lokacin, inda ta samu nasarar da take matukar bukata daga kwallayen da Tammy Abraham and Cesar Azpilicueta suka ci mata a kashin farko na wasan.

Abraham mai shekara 22, shi ne ya fara daga raga da bal dinsa ta 13 a kakar bana bayan minti 19 da shiga fili, bayan da Willian ya cilla masa wata kwallo.

Wannan bal da Abraham ya ci ta sa ya zama dan wasan Ingila na farko da ya taba ci wa Chelsea kwallo 13 a gasa a kaka daya kacal, tun bayan Lampard da ya ci mata 17 a kakar 2012-13.

Abraham din yana da damar wuce Lampard a wannan bajinta, kasancewar a yanzu ko rabin kakar ba a yi ba.

Tammy Abraham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hukuncin hana Chelsea sayen 'yan wasa ne ya sa Abraham ya samu damar yi wa kungiyar wasa sosai har tauraruwarsa take haskawa

Minti goma kafin tafiya hutun rabin lokaci sai kuma Azpilicueta ya ci ta biyu da ka daga bugun gefe da Emerson ya dauko, wanda hakan ya sa kungiyar ta Premier gaba da ci biyu ba ko daya a kashin farko na wasan.

Hankalin 'yan Chelsea ya tashi lokacin da tsohon dan wasanta na gaba Loic Remy ya ci wa Lille kwallo daya a minti na 78, amma suka yi kokari suka hana bakin yi musu kancal, inda suka tsallake zuwa matakin nag aba na gasar a bayan Valencia ta daya a rukuninsu, amma kuma a gaban Ajax, wadda ta kai wasan kusa da karshe a kakar bara.

Bayan kammala wasan rukunin nasu na 8, (Group H), Valencia wadda ta bi Ajax har gida ta doke ta 1-0, tana da maki 11 da yawan kwallo 2, Chelsea na bi mata baya ita ma da maki 11 da yawan kwallo 2.

Ajax, wadda ta ga samu ta ga rashi ta yi waje a matsayi na uku da maki 10 da yawan kwallo shida, yayin da Lille ta kasance ta karshe da maki daya da bashin kwallo 10.

Za a fitar da jadawalin wasannin mataki na gaba na gasar ta Zakarun Turai, a ranar Litinin, a birnin Nyon, na Switzerland da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya.

Tarihin da aka kafa a wasan:

Da wannan nasara da Chelsea ta samu, Lampard ya zama kociya dan Ingila na farko da ya kai wata kungiya matakin gaba na sili-daya-kwale na gasar ta Zakarun Turai, bayan da ya karbi jan ragamar dukkanin wasanni shida na rukuni na kungiyar, tun bayan da Harry Redknapp ya yi wannan bajinta da Tottenham a kakar 201-11.

Maki daya kawai Lille ta samu a wannan kaka da ta zamar mata mafi muni a matakin rukuni na gasar ta cin Kofin Zakarun Turai na Champions League.

Kungiyar ta Lille ta yi wasa shida a gidan kungiyoyin Ingila a manyan gasar Turai kuma ba ta taba yin nasara a ko da daya ba.

Loic Remy ya zama dan wasa na bakwai da ya ci wa Chelsea bal kuma ya ci kungiyar a filinta na Stamford Bridge a gasar ta Zakarun Turai ta Champions League, bayan Samuel Eto'o da Fernando Torres da Diego Costa da Michael Ballack da David Luiz da kuma Willian.