Ilimi na fuskantar koma baya a Afirka

An wallafa

Wani bincike da gidauniyar Mo Ibrahim ta gudanar ya nuna gwamnatocin kasashen Afirka sun gaza bunkasa harkar ilimi inda aka samu raguwa matuka cikin shekara biyar.

Binciken ya kuma gano yadda 'ya'yan da suka fito daga iyalai matalauta, ba sa samun damar zuwa kwalejin ilimi da jami'o'i, hakan ke janyo mutane ke gararanba da rasa aikin yi.

Haka kuma binciken ya yi hasashen lamarin zai munana sakamakon tsakanin matasan Afirka 'yan shekara 15.

Rahoton ya nuna an samu dan ci gaba ta fannin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki a kasashen Afirka, duk da cewa shugabanni sun gagara bunkasa tattalin arzikin da zai bai wa al'uma fatan samun sauyi.