Sudan: Al-Bashir zai bayyana gaban shari'a

A cikin makon gobe ne za a fara shari'ar tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir wata biyu bayan hambaras da shi daga kan mulki.
Shugaba Al-Bashir ya bayyana karon farko cikin bainar jama'a a ranar Lahadi, tun bayan hambarar da mulkinsa a watan Afrilu. An tuka shi cikin kwambar motoci da tsattsauran matakin tsaro daga gidan yari zuwa ofishin mai gabatar da kara.
Alaeddin Dafaallah Ali Abdeljader na sashen yaki da cin hanci rashawa a ofishin mai gabatar da karar ya tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon shugaban da suka dogara kan shadara ta biyar, da tara wadda ta shafi mallakar kudaden waje da kuma shadara ta shida game da tara dukiya ta haramtacciyar hanya.
Ana kuma tuhumar Omar al-Bashir da hannu a kisan masu zanga-zangar da suka gudanar da maci tsawon watanni don nuna adawa da mulkinsa na shekara talatin. An dai ci gaba da wannan zanga-zanga tun bayan kwace mulkin da sojoji suka yi.
A farkon wannan wata ma wasu jami'an tsaro sun sake kashe gomman masu zanga-zanga. Abin da mataimakin shugaban majalisar mulkin soja ta Sudan, Mohamed Hamdan Dagalo ya bukaci jama'a su dakaci sakamakon wani bincike a kan lamarin.
Tarzomar dai ta janyo tofin Allah tsine daga kasashen duniya, inda kungiyoyin 'yan adawa suka nemi sojoji su mika iko hannun gwamnatin farar hula. Mutumin wanda suke kira Hemedti ya yi jawabi ga shugabannin al'umma a taron da aka a ranar Lahadi.
Ya kuma musanta aikata ba daidai a lokacin tarzomar da ta auku ga masu zaman dirshen a wannan wata, tare da alkawarta cewa duk wadanda aka samu da hannu, za su fuskanci hukunci.
Sai dai shaidu da dama sun zargi rundunarsa da haddasa tarzomar, ya yin da kungiyoyin masu zanga-zanga sun kuma bukaci gudanar da bincike mai zaman kansa, maimakon wanda mutumin da ake zargi yake gudanarwa.












