Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona da Real Madrid sun yi canjaras 2-2
Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya saka kwallo ta biyu a ragar Barcelona, wanda ya sa kugiyoyin suka tashi a wasansu na "El Classico" da ci 2 da 2.
Tun da farko Barcelona ta buga da 'yan wasa 10 na tsawon mintuna 45, kuma saura wasanni uku kungiyar ta shafe dukkan kakar wasa ta bana ba a ci ta ba.
Alkalin wasa ya nuna wa Sergio Roberto jan kati a lokacin wasan yana 1 - 1 kafin a tafi hutun rabin lokaci bayan da alama ya mari dan wasan baya na Real Marcelo.
Amma da farko Roberton ne ya samar da kwallon da Luis Suarez ya jefa a ragar Real kafin Cristiano Ronaldo ya farke cin da Karim Benzema ya yi masa hedin.
Daga baya Lionel Messi ya saka kwallo ta biyu a ragar Real, amma sai Gareth Bale ya farke ta ba tare da bata lokaci ba.
An sauya Ronaldo a lokacin hutun rabin lokaci bayan da ya sami rauni a agararsa a lokacin da ya zura kwallon da ya ci.