Barcelona da Real Madrid sun yi canjaras 2-2

Lionel Messi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Lionel Messi ne kan gaba a La Liga da kwallo 33 a kakar wasan bana
An wallafa

Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya saka kwallo ta biyu a ragar Barcelona, wanda ya sa kugiyoyin suka tashi a wasansu na "El Classico" da ci 2 da 2.

Tun da farko Barcelona ta buga da 'yan wasa 10 na tsawon mintuna 45, kuma saura wasanni uku kungiyar ta shafe dukkan kakar wasa ta bana ba a ci ta ba.

Alkalin wasa ya nuna wa Sergio Roberto jan kati a lokacin wasan yana 1 - 1 kafin a tafi hutun rabin lokaci bayan da alama ya mari dan wasan baya na Real Marcelo.

Amma da farko Roberton ne ya samar da kwallon da Luis Suarez ya jefa a ragar Real kafin Cristiano Ronaldo ya farke cin da Karim Benzema ya yi masa hedin.

Daga baya Lionel Messi ya saka kwallo ta biyu a ragar Real, amma sai Gareth Bale ya farke ta ba tare da bata lokaci ba.

An sauya Ronaldo a lokacin hutun rabin lokaci bayan da ya sami rauni a agararsa a lokacin da ya zura kwallon da ya ci.

Cristiano Ronaldo scores for Real Madrid against Barcelona

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Cristiano Ronaldo da Alfredo Stefano ne ke da kwallaye 18 ga kowannensu a wasannin El Classico