Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Eddie Nketiah: Dan kwallon Ingila zai ci gaba da taka leda a Gunners
Dan kwallon Arsenal, Eddie Nketiah ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar, domin ci gaba da taka lerda a Gunners.
Tun farko kwantiraginsa zai kara a Emirates a karshen watan nan, wanda ya buga wasa 92 da cin kwallo 23, tun bayan da ya fara buga tamaula a kungiyar a 2017.
Ya taka rawar gani daga karshen kakar da aka kammala a Arsenal, wanda ya buga wasa takwas da suka raga da cin kwallo biyar.
Dan kwallon zai sa riga mai lamba 14, bayan da ya yi amfani da mai lamba 30 a baya.
Nketiah, ya fara da cin Norwich City kwallo biyu a Caraboa Cup a wasansa na farko a 2017, yana cikin jerin 'yan wasan Gunners da suka lashe FA Cup da Community Shield a 2020.
Dan wasan shi ne kan gaba a tawagar matasan Ingila 'yan kasa da shekara 21, mai kwallo 16 a raga a fafatawa 17 da ya yi mata.
Haka kuma shi ne kyaftin a tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 21 da ta lashe kofin nahiyar Turai na matasa a 2021.