Alexandre Lacazette: Dan wasan Arsenal ya sake koma wa Lyon

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Dan kwallon Arsenal, Alexandre Lacazette ya sake koma wa Lyon, shekaru biyar bayan ya hade da Gunners a kan fan miliyan 46 da rabi.
Lacazette ya koma kungiyar ta Faransa a kan yarjejeniyar shekaru uku har zuwa watan Yunin 2025.
Dan wasan Faransa mai shekaru 31, ya zura kwallo 54 a wasa 158 da ya buga wa Arsenal, sanna kuma ya taimaka mata lashe gasar FA Cup a shekara ta 2020.
A hirarsa da tashar Canal Plus a watan Afrilu, Lacazette ya ce "suna tuntubar juna" tsakaninsa da Lyon.

Asalin hoton, Getty Images
Lacazette ya kasance kyaftin din Arsenal bayan da Pierre-Emerick Aubameyang, ya koma Barcelona.






