Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Lacazette zai bar Arsenal nan da ƙarshen watan Yuni
Dan kwallon Faransa, Alexendre Lacazette zai bar Arsenal idan kwangilarsa ta kare a kungiyar a ranar 30 ga watan Yuni.
Dan shekaru 31, Lacazette ya koma Gunners ne daga Lyon a watan Yulin 2017.
Lacazette ya zura kwallo 71 cikin wasanni 206 da ya buga wa Arsenal kuma ya lashe gasar cin kofin FA a shekara ta 2020.
"Laca ya taka rawar gani sosai," in ji kocin Arsenal Mikel Arteta.
"Ya kasance hazikin dan wasa wanda ya taimaki matasan 'yan kwallo."
Lacazette ya ci ƙwallo shida sannan ya taimaka aka ci takwas a wasa 36 da ya buga wa Arsenal a kakar wasa ta 2021-22.
Ya jagoranci ƙungiyar a cikin fili bayan ƙwace kyaftin daga hannun Pierre-Emerick Aubameyang a watan Disamba saboda ladaftarwa.
"Ina so na ci gaba da tuna dukkan lokuta masu daɗi da na samu a ƙungiyar saboda a wajena abin alfahari ne na buga wa kulob ɗin da, tun ina yaro na fata, wasa," kamar ya faɗa wa shafin intanet na Arsenal a kwanan nan.
"Ina murna matuƙa da na samu damar buga wasa tsawon shekara biyar a Arsenal."