PSG ta kammala mallakar Nuno Mendes daga Sporting

Asalin hoton, PSG FC
An wallafa
Nuno Mendes ya saka hannu kan kwantiragin kaka hudu a Paris St Germain, bayan da ta biya kunshin yarjejehiyarsa a Sporting.
Tun farko dan kwallon ya koma buga wasannin aro a PSG a bara daga Sporting Lisborn, lokacin da Lionel Messi ya bar Barcelona da Sergio Ramos ya hakura da Real Madrid ba don yana so ba.
Bayan da Messi da Ramos suka kasa taka rawar gani a kakar farko a PSG, shi kuwa Mendes ya yi abin azo-a-gani a kungiyar da ta dauki league 1 na kakar nan.
Dan kwallon tawagar Portugal ya yi wasa 37 a dukkan karawa a PSG har 27 a Ligue 1 da wasa 18 da aka fara da shi a cikin fili - wanda ya samu damar-makin cin kwallaye sau 19.








