Jurgen Klopp ne gwarzon kungiyar masu horar da tamauala a bana

Jurgen Kloop

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An bayyana kociyan Liverpool, Jurgen Kloop a matsayin gwarzon kungiyar masu horar da kwallon kafa na bana.

Dan kasar Jamus mai shekara 54 ya karbi kofin da aka sa sunan Sir Alex Ferguson, wanda mambobin kungiyar koci-koci da ke horar da tamaula a Ingila kan zaba duk shekara.

Daman can Klopp ne ya lashe kyautar gwarzon mai horar da tamaula a Premier League a kakar nan, duk da Liverpool ba ta samu damar lashe kofin bana ba.

Manchester City ce ta yi nasarar daukar babbar gasar tamaula ta Ingila a kakar nan a ranar karshe da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool ta biyu.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta mata, Emma Hayes, ita ce ta lashe kyautar gwarzuwar mai horar da tamaula a Ingila a kakar nan.

Chelsea ce ta lashe babbar gasar tamaula ta Ingila ta mata kuma karo uku a jere, sannan ta dauki FA Cup na bana, bayan doke Manchester City 3-2.

Kloop ya ja ragamar Liverpool ta dauki FA Cup da League Cup a kakar nan - za ta buga wasan karshe a Champions League da Real Madrid ranar 28 ga watan Mayu a Faransa.

Koci-koci da suka yi takarar kyautar gwarzon Premier League a kakar nan, sun hada da na City, Pep Guardiola da na Brentford, Thomas Frank da na Newcastle, Eddie Howe da na Crystal Palace, Patrick Vieira.