Brahim Diaz ya zama matashin da ya ci Premier da La Liga da Serie A

Asalin hoton, Reuters
Brahim Diaz ya zama matashin dan kwallon da ya lashe kofi uku a babbar gasar tamaula uku manya a Turai.
Mai shekara 22, wanda ke buga wasan aro a AC Milan daga Real Madrid ya lashe Serie A ranar Lahadi, bayan da Milan ta doke Sassuolo 3-0.
Kofin farko da Milan ta dauka kuma na 19 jumulla, sannan a karon farko tun bayan kaka 10 ta tamaula, rabon da ta dauki Serie A.
Milan ta zama ta daya a kan teburin Serie A na kakar nan da tazarar maki biyu tsakaninta da Inter Milan abokiyar hamayya.
Bayan Serie A da Diaz ya dauka ya taba lashe La Liga da Premier, hakan ya sa ya zama matashin da ya yi wannan bajintar, bayan Cristiano Ronaldo da kuma Danilo.
Ronaldo, ya dauki Premier League a Manchester United a Ingila da kuma La Liga a Real Madrid a Sifaniya da daukar Serie A tare da Juventus a Italiya.
Shi kuwa Danilo ya dauki La Liga a Real Madrid a Sifaniya da Premier League a Manchester City a Ingila da kuma Serie A da ya lashe a Juventus a Italiya.
Brahim ya koma buga babbar gasar tamaula ta Ingila a 2017/18, ya kuma yi nasarar cin La Liga a Real Madrid, wadda ya yi wa wasa shida da cin kwallo daya.
Brahim mai shekara 22 da wata tara da kwana 20 ranar Litinin ya lashe kofin La Liga da Serie A da kuma Premier League a matakinsa na matashi.









