Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Mane, Elneny, Osimhen, Tielemans, Coutinho, Pepe, da Milinkovic
Newcastle United ta tuntubi Philippe Coutinho a kokarinta na dakile yunkurin Aston Villa na siyan dan wasan tsakiyar na Brazil mai shekara 29 a kan yarjejeniyar dindindin daga Barcelona. (Goal)
West Ham na shirin zawarcin dan wasan Aston Villa da Ingila Ollie Watkins, mai shekara 26 a bazara, inda kulob din ya bukaci a biya fam miliyan 50. (Guardian)
Barcelona na zawarcin dan wasan gaban Liverpool Sadio Mane, wanda ake alakanta shi da Bayern Munich. Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan mai shekara 30 dan kasar Senegal yana sha'awar komawa Nou Camp domin inganta damarsa ta lashe kyautar Ballon d'Or. (Mundo Deportivo)
Haka kuma Barca a shirye take ta ba kyaftin din Chelsea Cesar Azpilicueta albashin fam miliyan 11 a shekara, (Goal)
Leicester City na sa ran dan wasan Belgium Youri Tielemans zai bar kulob din a bazara kuma sun shirya don sauraron tayin fan miliyan 40 kan dan wasan mai shekara 25, wanda kwantiraginsa zai kare a bazarar 2023. (90Min)
Arsenal na daya daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin Tielemans, sai dai fatansu na siyanshi ya dogara ne a kan ko za su iya kammala gasar Premier a matsayi na hudu da samun damar shiga gasar zakarun Turai. (Standard)
Manchester United da Newcastle United suna sha'awar sayen dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen amma Napoli na son akalla Yuro miliyan 100 kan dan wasan mai shekara 23. (Calciomercato)
Sevilla za ta iya sayen dan wasan gefe na Arsenal Nicolas Pepe, mai shekara 26, a bazara, inda dan wasan na Ivory Coast ya kai kusan fan miliyan 25. (Super Desporte)
Shugaban Lazio Claudio Lotito ya ce ya ki amincewa da tayin Yuro miliyan 140 kan dan wasan tsakiyar Serbia Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27, wanda Manchester United da Paris St-Germain ke nema. (Real Sport)
Manchester United a shirye take ta biya fam miliyan 38 na sayen dan wasan bayan Sporting Lisbon dan kasar Portugal Goncalo Inacio, mai shekara 20. (A Bola)
Dan wasan Faransa Paul Pogba zai rage albashi idan ya koma kungiyar Juventus ta Italiya idan kwantiraginsa a Manchester United ya kare a bazara. Paris St-Germain ta kara tayin dan wasan mai shekara 29, yayin da Real Madrid ke sa ido kan yanayin dan wasan. (Alfredo Pedulla)
AC Milan na zawarcin dan wasan bayan Arsenal da Faransa William Saliba, mai shekara 21, wanda ke zaman aro a Marseille. (Mirror)
Duk da rahotannin da ke cewa Gunners ta fara tattaunawa da dan wasan tsakiya na Masar, Mohamed Elneny, mai shekara 29, rahotanni na cewa ya amince da yarjejeniya da Galatasaray. (Fanatik)
Da alama Tottenham za ta iya doke Manchester United wajen sayen golan West Bromwich Albion Sam Johnstone, mai shekara 29. Dan wasan na Ingila, wanda ya fara taka leda a Old Trafford, zai kasance yana dafa wa Hugo Lloris a Spurs. (Standard)
Spurs din kuma suna tunanin bai wa tsohon dan wasan Manchester City da Ivory Coast Yaya Toure, mai shekara 38, mukamin (Standard)
Manchester United na gab da kulla yarjejeniya da mataimakin kocin Ajax Mitchell van der Gaag don komawa kungiyar don taimaka wa Erik ten Hag a Old Trafford (Fabrizio Romano).