Barcelona vs Celta Vigo: 'Yan Barca da za su kara da Celta

Barcelona Fc

Asalin hoton, Barcelona FC

An wallafa

Celta Vigo ta ziyarci Barcelona, domin buga wasan mako na 36 a gasar La Liga da za su fafata ranar Talata a Camp Nou.

Kungiyoyin biyu sun kara a wasan farko a bana a gasar ta La Liga ranar 6 ga watan Nuwambar 2021, inda suka tashi 3-3 a gidan Celta.

Celta ta ci kwallayen ta hannun Nolito da kuma Iago Aspas da ya zura biyu a raga a fafatawar.

Ita kuwa Barcelona ta ci kwallayen ta hannun Ansu Fati da Sergi Busquets da kuma Memphis Depay.

Barcelona wadda tuni ta samu gurbin buga gasar Champions League ta badi tana ta biyu a teburin La Liga da maki 69.

Ita kuwa Celta mai maki 43 tana ta 11 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta ta Sifaniya ta kakar nan.

Kungiyar Real Madrid tuni ta lashe La Liga na bana kuma na 35 jumulla tana da maki 81 kawo yanzu, saura wasa uku-uku a karkare kakar nan.

Tuni kociyan Barcelona, Xavi ya bayyana 'yan wasa 23 da zai fuskanci Celta a Camp Nou ranar Talata.

'Yan wasan Barcelona:

Ter Stegen, R. Araujo, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Memphis, Ansu Fati, Adama, Braithwaite, Neto, Lenglet, L. De Jong da kuma, Jordi Alba.

Sauran sun hada da Ferran, F. De Jong, O. Mingueza, Umtiti, Eric, Aubameyang, Gavi, Álvaro Sanz, Arnau Tenas da kuma Jandro.