Kasuwar 'yan ƙwallo: Makomar Terling, Mane, Pogba, Haaland, Oxlade-Chamberlain, Adeyemi

dd

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta shirya gwada sa'arta kan saye ɗan wasan Ingila Raheem Sterling idan Manchester City ta amince ta sayar da ɗan wasan mai shekara 27 a wannan kakar, akwai sauran shekara guda a kwantiraginsa. (Telegraph - subscription required)

Gunners ta soma tattaunawa da ɗan wasan Masar mai shekara 29 da ke buga tsakiya Mohamed Elneny, wanda kwantiraginsa na yanzu da ita ke karewa a wannan kakar. (Athletic - subscription required)

Bayern Munich na shirin gwada sayen ɗan wasan Liverpool da Senegal da ke buga gaba Sadio Mane, mai shekara 30, tuni dai ƙungiyar ta Jamus ta tuntubi wakilan ɗan wasan. (Sky Germany via Metro)

Alex Oxlade-Chamberlain na Liverpool mai shekara 28, na fargabar makomarsa a ƙungiyar, ganin har yanzu ba a tuntube shi a kan sabon kwangila kuma rabonsa da ya yi wasa tun 20 ga watan Maris. A kaka mai zuwa kwantiragin ɗan wasan tsakiyar ke karewa.. (Mail)

Ɗan wasan Faransa da ke buga tsakiya Paul Pogba, wanda kwantiraginsa da Manchester United ke karewa a karshen kaka, ya shaidawa Manchester City cewa ba shi da ra'ayin taka mata leda, yayinda ake tunanin ɗan wasan mai shekara 29 na son tafiya wata ƙungiyar ce ta daban. (Athletic, via Mirror)

Kocin Chelsea Thomas Tuchel na sa ran ya samu goyon-bayan sabon mutumin da zai mallaki kungiyar. (Telegraph - subscription required)

Kocin Newcastle United Eddie Howe zai saurari tayi kan 'yan wasa kusan 10 a karshen kakarna, ciki har da Kyeftin Jamaal Lascelles. (Sun)

Ɗan wasan Chelsea Jake Clarke-Salter, mai shekara 24, ana zawarcinsa a Leeds United da PSV Eindhoven bayan taka rawar gani a zaman aron da ya yi a Coventry City.(Sun)

Kocin Barcelona Xavi ya ce matsalolin kuɗi ya sa sun gaggara iya dauko ɗan wasan nan mai shekara 21 da suka jima suna zawarci Erling Haaland, wanda yanzu zai koma Manchester City daga Borussia Dortmund. (ESPN)

Ɗan wasan Red Bull Salzburg da Jamus Karim Adeyemi, mai shekara 20, na gab da komawa Borussia Dortmund bayan Manchester United ta gaza daidaitawa da shi. (Metro)

Sunderland na kitsa yada za ta dauko Jobe Bellinghma - ƙani ga ɗan wasan Borussia Dortmund da Ingila, Jude - daga Birmingham.(Mail)

Kulob din Birmingham City na gab da zaman mallakin wani attajirin Burtaniya. Sai dai kujerar kocin kungiyar Lee Bowyer, na fuskantar barazana. (Telegraph - subscription required)

Middlesbrough na shirin bai wa mai tsarin raga asalin Ingila Joe Lumley, mai shekara 27, da Luke Daniels, mai shekara 34, damar bankwana da ita, dukkanin 'yan wasan biyu dai na da sauran kwantiragin shekara ɗaya da kulob din. (Football Insider)