Mikel Arteta zai ci gaba da jan ragamar Arsenal zuwa 2024-25

An wallafa

Mikel Arteta ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar Arsenal zuwa karshen kakar 2024-25.

Arteta ya fara horar da Arsenal ranar 23 ga watan Disambar 2019, kawo yanzu ya ja karawa 127 a dukkan fafatawa da cin 69 da canjaras 22 da rashin nasara a wasa 36.

Haka shima kociyan kungiyar kwallon kafa ta mata ta Arsenal, Jonas Eidevall ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da horar da Gunners.

Eidevall ya koma Arsenal da horar da tamaula a bara, yanzu zai ci gaba da aiki zuwa karshen kakar 2023-24.

Kawo yanzu Arteta ya kai Arsenal mataki na hudu a kan teburin gasar Premier a bana da tazarar maki biyu tsakani da Tottenham ta biyar.

Arsenal tana fatan samun gurbin buga gasar zakarun Turai ta Champions League a badi, wadda ba ta samu shiga fafatawar bana ba.