Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Rashford, Lingard, Gabriel, Lewandowski, Neves, Tielemans, Jorginho, Rice

r

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ana rade-radin cewa dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 24, ba zai bar Manchester United ba, amma kuma dole a yanzu ya nuna wa sabon kocinsu Erik ten Hag irin hikimarsa. Shi ma ɗan wasan tsakiya Jesse Lingard, mai shekara 29, na iya ci gaba da zama a kungiyar. (Sun)

Ɗan wasan Arsenal Gabriel Magalhaes, mai shekara 24, shi ne mutumin da a yanzu Juventus ta Italiya ke son dauka. (Gianluca Di Marzio, via Teamtalk)

Darakta a Barcelona Mateu Alemany ya musanta cewa sun gana da wakilan ɗan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski kan ya koma taka musu leda. (Movistar, via Goal)

Ɗan wasan tsakiya a Belgium Youri Tielemans, wanda ke da kwangila da Leicester City har zuwa 2023, zai so ya koma Sifaniya idan ya yi ban-kwana da kulob din. Ana kuma rade-radin cewa Real Madrid na zawarcinsa. (Sacha Tavolieri, via Mail)

Ana alakanta dan wasan tsakiya a West Ham Declan Rice da Chelsea, Manchester City da Manchester United sai dai ɗan wasan, mai shekara 23, ya ce a yanzu ba zai yarda irin wadannan maganganu su ja hankalinsa ba .(Sky Sports News)

Manchester United ta aike tawaga domin kallon wasan ɗan wasan Portugal mai buga tsakiya Ruben Neves a Wolves a wasan da aka ci su 3-0 a fafatawa da Brighton ranar Asabar. Kungiyar da ke Old Trafford ta ce tana son aiki da ɗan wasan mai shekara 25. (Birmingham Live)

Juventus ta gabatar wa Chelsea tayi ɗaukar ɗan wasanta na tsakiya Jorginho.A shekarar 2023 kwantiraginsa zai kare a Blues. (Todofichajes - in Spanish)

Marcos Alonso da ke buga baya a Chelsea na daga cikin zabin da Barcelona ke son dauka a yanzu. (Fabrizio Romano, via Marca)

Napoliita ma ta shiga zawarcin ɗan wasan Chelsea Armando Broja, bayan ya burge ta a lokacin zamansa na aro a Southampton. (Todofichajes - in Spanish)

Kocin riƙon-ƙwarya a Reading Paul Ince, wanda ya faɗa a kasan layi a wannan kakar a teburin Championship, zai tattauna da mai kungiyar a wannan makon, Dai Yongge, kan makomarsa. (Berkshire Live)