Liverpool da doke Newcastle ta koma ta daya a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool na kara buda fukafukansu a yakin lashe gasar Premier bayan sun cinye Newcastle nasara ta hudu da suka samu ke nan a jere, za su hau saman tebur a kalla na wasu awanni kan City ta yi wasa.
Sauye-sauye biyar Jurgen Klopp ya yi a filin wasa na St James' Park, ciki har da barin Mohamed Salah a benci saboda wasan dab da na karshe da za su buga a Champions a ranar Talata.
Da farko Newcastle ta bude wuta sosai, dama a yan kwanakin nan tana kokari, abin da ya tilasta Liverpool yin kuskure daga farkon wasan.
Amma daga baya Liverpool ta mamaye wasan kuma Naby Keita ya jefa kwallo a ragar Newcastle a minti na 19.
Dan wasan sai da ya shiga yadi na 18 ya yanka mai tsaron raga Martin Dubravka kafin ya ci kwallon.
Liverpool ta samu damarmaki masu yawa amma ba a sau damar jefa kwallo ta biyu ba, duk da yake Liverpool dai ta samu sha da wannan maki
Amma ba zaman teburi ba ne na dindindin, duk da cewa sun yi abin da ya kamata, amma idan City ta yi wasa za a ga inda aka dosa a gasar.






