Kasuwar ƴan ƙwallo: Guardiola, Ward-Prowse, Torres, Haaland, James, De Jong, Dembele, Reguilon

An wallafa

Manchester City na da yaƙinin Pep Guardiola zai sanya hannu a sabon kwantiragin ci gaba da zama da ita a sabuwar kaka, yayinda ake kan tattaunawa kan tsawaita zamansa a ƙungiyar har shekara ta 2025.(Sunday Mirror)

Manchester City da Manchester United na son dauko ɗan wasan Ingila mai buga tsakiya James Ward-Prowse daga Southampton, yayin da Arsenal, Newcastle United da Tottenham ke sanya ido kan ci gaban da ake samu a tattaunawa da matashin ɗan shekara 27. (Daily Star on Sunday)

Manchester City da Manchester United na kuma tataɓurza kan saye ɗan wasan Sifaniya mai buga tsakiya Paul Torres, ɗan shekara 25, daga Villarreal. (Todofichajes - in Spanish)

Erik ten Hag, wanda ke bankwana da Ajax domin soma horas da Manchester United a karshen kaka, na son ya sayo ɗan wasan Feyenoord da Netherlands Tyrell Malacia, mai shekara 22. (Sunday Mirror)

Shugaban ƙungiyar Borussia Dortmund Hans-Joachim Watzke ya ce ƙungiyar ta doke Manchester United wajen cimma yarjejeniya da Erling Haaland a Disambar 2019, saboda tsarinsu na ba shi damar tafiya a cikin kwantiragin da aka cimma da ɗan wasan mai shekara 21. (Goal)

Chelsea za ta gabatar da tayi ƙan Reece James mai shekara 22, wanda ake ta alakantawa da Real Madrid. (90 Min)

Mai buga tsakiya Frenkie de Jong ana cewa zai tafi Manchester United amma kocin Barcelona Xavi ya ce ɗan wasan mai shekara 24 shi ne makomar ƙungiyar ta Sifaniya a yanzu da kuma a gaba. (Manchester Evening News)

Ɗan wasan da ke buga gaba a Faransa Ousmane Dembele, mai shekara 24, ya samu tayi mai gwaɓi daga Paris St-Germain sama da abin da Barcelona ke ba shi, amma dai ya fi son ya ci gaba da zama a Nou Camp a yanzu. (Sport)

Real Madrid za ta bukaci euro miliyan 40 wajen sayo Sergio Reguilon daga Tottenham. (Todofichajes - in Spanish)

Wolves a shirye take ta sayar da ɗan wasanta mai shekara 25 da ke buga tsakiya Ruben Neves. (Sunday Times - subscription required)

Everton na zawarcin ɗan wasan Ingila mai shekara 29 James Tarkowski, wanda kwantiraginsa ke karewa a Burnley wannan kakar. (Football Insider)

Crystal Palace, Watford da Fulham na sanya ido kan ɗan wasan FC Koln na Jamus Timo Hubers, wanda tuntuni ake cewa zai je Leeds United. (Football Insider)

Newcastle United ta gabatar da tayi kwantiragin shekara hudu kan ɗan wasan Ingila Sean Longstaff. (Sunday Times - subscription required)

AC Milan ta amince da yarjejeniyar Lille domin saye ɗan wasan Portugal Renato Sanches, mai shekara 24 da ke buga tsakiya kan, euro miliyan 20 (£16.8m). (Football Italia)

Ɗan wasan Netherlands mai tsaron baya Sven Botman, ana cewa zai je Newcastle United ko AC Milan.(Get French Football News)