Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona za ta koma buga wasa a Olympic Stadium daga 2023-24
Barcelona za ta koma buga wasanninta na gida a Olympic Stadium a 2023-24, bayan da za ta fara gyran filin Camp Nou.
Barcelona ta tabbatar a ranar Alhamis cewar za ta fara aikin bunkasa Camp Nou da zarar an karkare kakar bana, bayan da mahukuntan birnin suka amince da shirin.
Kashin farko da na biyu zai mayar da hankali wajen gyare-gyaren muhimman wurare da daga darajar fasahar ginin da za ta yi kafada da wannan zamanin.
Kaso na uku zai shafi rushe-rushen wurare da za a fara a karshen shekara, da nufin yadda yan kallo za suke cika filin makil daga farkon kakar 2024-25.
Hakan ne zai sa Barcelona ta koma buga wasannin gida a badi a Montjuic, maimakon Camp Nou, inda za ta ke karawa a katafaren filin da ya karbi bakuncin Olympic a 1992.
Filin zai dauki 'yan kallo 60,000 - kafin daga baya Barca ta koma Camp Nou a kakar 2024-25, amma sai a 2025-26 za a kammala komai.
Barcelona ta sanar cewar kudin aikin da za a yi zai kai Yuro bilyan 1.5