Barcelona: Za ta sauya sunan filin Camp Nou zuwa Spotify Camp Nou

An wallafa

Za a sauya sunan filin Barcelona zuwa Spotify Camp Nou, bayan da kungiyar ta Sifaniya ta cimma yarjejeniya da Spotify.

Sai dai kuma za a jira tabbatar da kwantiragin a babban taron da kungiyar za ta gudanar a Yuli.

Haka kuma za a rubuta sunan kamfanin na Sweden a gaban rigunan da 'yan wasa maza da na mata za suke amfani da su da kuma na atisaye.

Barcelona ta ce kwantiragin da suka cimma zai fara daga kakar 2022-23 zuwa kaka hudu.

Wannan shine karon farko da aka saka suna a gaban harafin Camp Nou a katafaren filin wasa na Barcelona mai cike da tarihi.

Kamar yadda kungiyar ta sanar yarjejeniyar da ta kulla da Spotify ta kai Euro miliyan 280.

A bara ne wanda ya kirkiro Spotify, Daniel Ek ya yi tayin sayen Arsenal mai buga Premier League, inda tsoffin 'yan wasan Gunners da suka hada da Thierry Henry da Dennis Bergkamp da kuma Patrick Vieira suka mara baya.