'Ralf Rangnick: Man United ba za ta yi shekara 30 ba tare da lashe Premier ba''

Liverpool vs Man United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mohamed Salah ya ci kwallo uku a wasan da Liverpool ta doke United 5-0 cikin watan Oktoba
An wallafa

Manchester United ba za ta yi shekara 30 ba tare da lashe kofin Premier League, kamar yadda Liverpool ta yi ba, in ji Ralf Rangnick.

Kocin rikon kwaryar ya ce United za ta bunkasa kungiyar wajen sayen fitattun 'yan wasa, domin ta lashe kofin nan kusa.

Rabon da United ta dauki Premier League tun 2013, za kuma ta ziyarci Liverpool domin buga Premier League ranar Talata.

Bayan da Liverpool ke fatan lashe kofi hudu a bana, ita kuwa United fatan ta kare a mataki na hudun farko take yi a kakar nan.

Hakan ne zai sa ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta badi, wato Champions League.

''Muna bukatar kara bunkasa kungiyar don harin gaba,'' in ji Rangnick.

''Bana jin za mu yi kaka 30 ba tare da lashe Premier League ba, hakan zai yi wahala, kuma mune za mu hana hakan.''

Liverpool wadda ta casa United 5-0 a gasar Premier League ta bana, ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Ingila a 2020, hakan ya kawo karshen shekara 30 ba tare da dauka ba tun 1990.

Ana ta rade-radin cewar Erik Ten Hag ne zai maye gurbin Rangnick, kuma nan kadan ake sa ran United za ta sanar da daukar mai horarwar kan yarjejeniyar kaka uku.

Idan har United ta dauki kociyan Ajax din, zai zama na biyar da kungiyar za ta dauka tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya.

Rangnick ya ce ''Idan har kasan ƴan wasan da kake bukata da kwazonsu da bajintarsu, sai kuma ka tsara yadda za ka kawo su kungiya, su kuma amince da abun da za ka sanar da su don cin gaban wasanninsu.''

Kocin rikon kwarya na Manchester United, Rangnick ya taka rawar gani a ƴan wasa shida a Liverpool.

Rangnick ya yi aiki tare da Roberto Firmino a Hoffenheim da Joel Matip a Schalke, haka kuma shi ne daraktan kwallon kafa a Red Bull a lokacin da kungiyar ta dauko Sadio Mane da Naby Keita da Ibrahima Konate da kuma Takumi Minamino.