'Ko dai ba su iya komai ba ko kuma ba su damu da United ba'

BBC
An wallafa

'Yan wasan Manchester United d yawa 'Ko dai ba su da iya komai ba ko kuma ba su damu da United ba'

Tsohon dan wasan kungiyar Peter Schmeichel na daya daga cikin wadandfa ba su ji dadin abin da ya faru ba ga kungiyar a ranar Lahadi a wasan hamayyar da City ta doke United da ci 4-1.

Kevin de Bruyne da Riyad Mahrez sune kowanne cikinsu ya ci kwallo biyu, a wasan da Jadon Sancho ya farke wa Ralf Rangnick da United aka yi 1-1.

Babu abin da United ta yi a wasan, wanda sau daya ta buga wa mai tsaron ragar City Ederson kwallo ya tare, ko da yake ya kamata a zura musu kwallaye sama da 4 - bayan kwallon da phil Fiden ya buga ta daki turke da kuma damarmakin da suka barar.

Tsohon dan wasan United din wanda kuma ya bugawa City Schmeichel, ya ce " Na yi tsammanin Rangnick zai sauya salon kwallon da ake bugawa bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Da ya samu abin fada amma mintina 45 na biyu ba su yi kyan gani ba. A duka lokacin babu abin da ya nuna United za ta iya sa ko kwallo guda.

"Akwai 'yan wasa da dama da ko dai ba su iya komai ba, ko kuma ba su damu da kungiyar ba. kocin rikon kwarya ba zai iya yin abubuwa da yawa ba. Ya san cewa ba shi zai ci gaba da rike kungiyar ba, me zai yi?

"Manchester City sun bunkasa, dan haka ba su matsa lamba kan sai sun cinye United ba, da sai abin ya fi bata wa United rai."

'Bai kamata su buga wa Unietd wasa ba'

Abokan taka ledar Schmeichel a United, Roy Kean da Gary Neville sun bayyana irin wannan ra'ayi a gidan talabijin na Sky Sports.

Kean ya ce: "United ta karaya a wannan wasan hamayyar, ba abin a yafe ba ne ko a dauke kai.

"Zan iya dauke kai game da kurakurai, amma ba koma wa baya ba a tare, ba wai kokari suke yi ba kare hare-hare ba - akwai 'yan wasan da bai kamata su bugawa United wasa ba kwata-kwata ba.

"Duk muna rashin nasara a kwallon kafa, amma yadda ake cinye kungiyar cikin sauki. Muna tsammanin za su fito wasan da burin samun nasara a kuma fusace.

"In ba za ka iya gwagwarmaya ba, kasa jikinka domin United kamata ya yi ka koma gefe kar ka janyo mana abin kunya", in ji Roy Kean.

Ya kuma zargi Fred da tsayawa kamar yana jiran mota maimakoman neman kwallo a ci na biyu da De Bruyne ya yi.

Reuters

Asalin hoton, Reuters

Sai dai kocin United ya mayar da martani a wata hira da ya yi da Sky Sports yana cewa "Ba zan iya tilasta 'yan wasa su yi abin da nake so ba".