Arsenal ta doke Watford ta koma matsayi na hudu

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta doke Watford har gida ta kuma koma matsayi na hudu saman Manchester United da maki daya.
Yanzu kungiyar ta koma matsayin kungiyoyin da za su iya zuwa gasar zakarun Turai Champions a shekara mai zuwa.
Ita kuma Watford tana nan a karkashin teburi jerin wadanda za su iya fadawa gasar Championship a 2023.
Martin Odegaard ne ya fara ci wa Arsenal kwallo a minti na biyar da fara wasan, kafin daga bisani Cucho Hernandez ya farkewa masu masaukin baki a minti na 11.
Bayan minti na 30 ana kunnen doki a wasan, Bukayo Saka ya kara sanya Arsenal a gaba, da kwallon da Lacazette ya ba shi ya ci.
An tafi hutun rabin lokaci Arsenal na kan gaba da ci 1-2 bayan kuma dawowa ne a minti na 52 Gabriel Martinelli ya kara zira ta uku in da shi ma Lacazette ya bashi kwallo ya ci.
Ana saura mintina kadan a kare wasan Moussa Sissoko ya kara ramawa Watford kwallo guda, abin da ya kai aka kammala wasan da cin kwallaye biyar.
Arsenal za ta ci gaba da zama a matsayi na uku ne idan wasan da za a buga tsakanin Manchester United da City bai yi wa United kyau ba.
Gunners yanzu haka na da wasannin hudu da ba ta yi ba a baya, wadanda idan ta samu nasarar cinye su baki daya to har matsayi na uku da Chelsea ta ke za ta dare.











