Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Carabao Cup: Liverpool ta lashe kofin bayan ta doke Chelsea a bugun finareti
Liverpool ta dauki kofin Carabao bayan ta doke Chelsea a wasan karshe a filin wasa na Wembley.
Bayan sun tashi babu ci daga farawa har zuwa minti na 120, wasan ya tafi bugun fenariti, kuma hakan ya sa Liverpool ta yi galaba da ci 11-10.
Mai tsaron ragar Chelsea, Kepa Arrizabalaga da ya shigo kafin bugun fenaretin, shi ne ya zubar da bugun karshe.
Dan wasan gaban Chelsea Romelo Lukaku ya ci kwallo a cikin wasa, amma na'urar da ke taimaka wa alkalin wasa ta VAR ta soke kwallon.
Wannan ne karon farko da Jurgen Klopp ya ci kofin Carabao tun zuwansa Liverpool.
Kuma shi ne kofin farko da Liverpool ta ci a cikin kofuna hudu da take da damar lashewa a bana.
Kafin wasan Liverpool ta bayyana cewa mai tsaron bayanta Kelleher na daga cikin matasan yan wasan Liverpool da suka taka rawa sosai a gasar, kuma ya cancanci ya shiga raga a yau.
Kuma sai ga shi ya ci wa kungiyar tasa kwallon da ta bata nasara a filin na Wembley.