Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abramovich ya hakura da tafiyar da Chelsea
Mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Roman Abramovich ya aminta ya bada ragamar gudanar da kulob din hannun kwamitin amintattu na 'Chelsea charitable foundation'.
Abramovich wanda zai cigaba da zama mamallakin kulob din ya dauki matakin ne yayin da Rasha ta kutsa Ukraine kuma ake ci gaba da yaki.
Matakin na kuma zuwa yayin da Chelsea ke buga wasan karshe na kofin Carabao da Liverpool a filin Wembley da ke London.
'' A ko da yaushe ina daukar matakin da ya yi dai-dai da bukatar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.''
'' Kuma zan cigaba da dabbaka wannan akida. Hakan ma ya sa a yau na aminta na mika wa gidauniyar 'Chelsea charitable foundation' ragamar ci gaba da gudanar da kungiyar.'' In ji Abramovich.
Ya kara da cewa '' ina ganin a wannan gabar sune ya kamata su tafiyar da kungiyar tun daga walwalar yan wasa da ma'aikata da magoya baya.''
Itama kungiyar ta Chelsea ta sanar a shafinta na internet cewa ''tana alla-wadai da abinda ke faruwa Ukraine.''
Kazalika kungiyar magoya bayan Chelsea ta ce suna bukatar cikakken bayani kan makomar kungiyar bayan kalaman Abramovich.
BBC ta fahimci cewa kungiyar ba ta sayarwa bace a halin yanzu, kuma babu batun biyan bashin da Abramovich ke binta da ya kai fam biliyan 1.5.
Abramovich wanda dan kasar Rasha ne na daga cikin hamshakan masu arzikin kasar da ke da alakar-kud-da-kud da Shugaba Vladimir Putin.
A farkon mako ne dan majalisar Burtaniya bangaren adawa Chris Bryant ya zarge shi da aikata cin hanci da rashawa a kasar, da kuma zargin gwamnati da yin gum da bakinta.
Hakama Mr Bryant ya bukaci a kwace kadarorinsa da ke kasar da suka hada da wani gidansa na fam miliyan 152.
Kofin Zakarun Turai da Chelsea ta ci bara na nufin babu wani kofi da ya rage wanda kulob din bai ci ba a karkashin Roman Abramovich.