Champions League 2022: UEFA ta ce za a buga wasan karshe a Paris a maimakon Rasha

The Gazprom Arena in St Petersburg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An gina filin wasa na Gazprom Arena a 2018 saboda gasar cin kofin
An wallafa

Za a buga wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai watau Champions League na bana a Paris, bayan da aka dauke daga Rasha saboda kutsen da kasar ta yi a Ukraine.

A baya an shirya buga wasan mafi girma a Turai a filin wasa na Gazprom Arena da ke St Petersburg a ranar 28 ga watan Mayu.

Amma a yanzu hukumar kwallon Turai - UEFA ta ce a filin wasa na Stade de France da ke Paris.

Hukumar Uefa ta nuna godiya ga shugaban Faransa, Emmanuel Macron saboda "nuna goyon baya da taimakon da yake bai wa kwallon kafa a Turai."

Hukumar ta kara da cewa "Tare da gwamnatin Faransa, Uefa za ta taimaka wajen ceto 'yan kwallo da iyalansu a Ukraine."

Shekaru uku kenan a jere da ake canza filin wasan da a baya aka tsara za a yi wasan karshen na gasar zakarun Turai.