Yayin da Ukraine ta fara fuskantar hare-hare daga Rasha, kungiyoyin kwallon kafa da dama sun nuna goyon baya ga Ukraine a lokacin wasanni Zakarun Turai na Europa da aka buga Alhamis da daddare.
Wasu daga cikin yan wasan da suka ci kwallo sun nuna riga dauke da kalaman bukatar zaman lafiya a Ukraine.
Ga jerin hotunan yadda yan wasan suka nuna goyon bayansu kan abinda ke faruwa a Ukraine din.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Yadda yan wasan Barcelona suka yi kira da a daina yaki gabanin fara wasansu da Napoli a filin wasa na Diego Maradona da ke Naples
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Kungiyar Zenit St Petersburg ce kawai daga Rasha a cikin gasar Zakarun Turai, kuma Real BVetis ta cire ta a daren na Alhamis
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Yan kallo na daga tutar Ukraine yayin wasan Celtic da Bodo a Norway
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Kungiyar Slavia Prague ta bai wa mai staron bayanta dan kasar Ukraine Taras Kacharaba kyaftin a wasansu da Fenerbache don nuna goyon baya
Asalin hoton, SK SLAVIA PRAGUE
Bayanan hoto, Taras Kacharaba
Asalin hoton, FOOTBALL SCOTLAND
Bayanan hoto, Magoya bayan kungiyar Bodo kenan ke daga launin tutar Ukraine don nuna goyon baya
Asalin hoton, ATALANTA B.C.
Bayanan hoto, Ruslan Malinovskyi dan Ukraine kenan da ke yaci wa Atalanta kwallo biyu da Olympiacos ya kuma nuna rigarsa da ke aka rubuta cewa ''ba ma bukatar yaki a Ukraine