Europa League: Barcelona na neman kofin da ba ta taɓa lashewa ba

An wallafa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona za ta fara fafatawa a wasannin gasar Zakarun Turai ta Europa League ranar Alhamis, gasar da ba taɓa lashewa ba a tarihi.

Barca za ta fara gasar ce a filin wasanta na Camp Nou a karawa tsakaninta da Napoli, yayin da mai horarwa Xavi Hernández zai buga wasansa na farko a gasar zakarun turai a matsayin koci.

Xavi ya ce sabon ɗan wasan gaba da ƙungiyar ta saya daga Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, "ya shiya tsaf don buga wasan".

"Duk da cewa ba zai taɓa zama madadin cire mu daga Champions League ba, wasan zai kasance mai zafi gare mu. Kofi ne da ba mu taɓa lashewa ba duk da cewa mun sha haɗuwa da shi ta wasu hanyoyi," a cewar ƙungiyar cikin wata sanarwa.

Barca ta buga gasar Europa sau 11 a baya amma ba ta zuwa wasan ƙarshe ba.

Daga Champions League zuwa Europa

Barcelona ta tsinci kanta a gasar Europa ne bayan da Bayern Munich ta lallasa ta da ci 3-0 a wasan ƙarshe na rukuni a Champions League a watan Disamba da ya gabata.

Wannan ne karon farko da Barca ta gaza shiga zagayen 'yan 16 na Champions League cikin shekara 17 - tun a 2003-2004 da ta gaza samun gurbin shiga gasar baki ɗayanta.

An ƙirƙiri gasar Europa ne a shekarar 1971/1972 a matsayin ta ƙungiyoyin da suka gaza samun shiga gasar European Cup ko Cup Winners' Cup ta hanyar kasa lashe kofunan cikin gida a ƙasashensu.

A 1999, an soke Cup Winners' Cup sannan aka mayar da Cup Winners cikin gasar UEFA Cup. Daga baya kuma aka sauya sunanta zuwa Europa League a 2008.

Duk da cewa ana kallon ta a matsayin "gasar gajiyayyu", wasu da yawa na ganin Europa League ta fi sauran wahalar lashewa saboda yawan ƙungiyoyi kuma waɗanda suka fito daga ƙasa ɗaya a wasu lokutan.