Afcon 2021: Kididdigar kammala zagayen farko da ya kamata ku sani a Afcon

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Ranar Alhamis aka karkare wasannin zagayen farko a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Kamaru gasa ta 33 a tarihi.

An samu kungiyoyin da suka kai zagaye na biyu su 16, yayin da takwas suka koma gida daga 24 da aka fara wasannin bana da su har da mai rike da kofin Algeria da Ghana mai tarihin lashe kofi.

Cin kwallaye

An ci kwallo 68 a wasa 36 bayan da aka kammala fafatawar zagayen farko da a kalla ake cin kwallo 1.89 a duk wasa.

Kwallo biyar a raga

  • Kyaftin din Kamaru, Vincent Aboubakar

Kwallo uku a raga

  • Dan wasan Mali, Ibrahima Koné

Cin kwallo biyu a raga

  • Dan wasan Kamaru, Karl Toko Ekambi
  • Dan wasan Comoros, Ahmed Mogni
  • Dan kwallon Gabon, Jim Allevinah
  • Dan wasan Gambia, Ablie Jallow
  • Dan kwallon Ivory Coast, Nicolas Pépé
  • Dan wasan Malawi, Gabadinho Mhango
  • Dan kwallon Morocco, Sofiane Boufal
  • Dan wasan Tunisia, Wahbi Khazri

Kungiyoyin da suka kai wasannin zagaye na biyu:

Rukunin farko:

  • Cameroon
  • Burkina Faso
  • Cape Verde

Rukuni na biyu:

  • Senegal
  • Guinea
  • Malawi

Rukuni na uku:

  • Morocco
  • Gabon
  • Comoros

Rukuni na hudu:

  • Najeriya
  • Masar

Rukuni na biyar:

  • Ivory Coast
  • Equatorial Guinea

Rukuni na shida:

  • Mali
  • Gambia
  • Tunisia

Wasannin zagaye na biyu da za a fara da kungiyoyi 16 daga ranar Lahadi

Lahadi 23 ga watan Janairu

  • Wasan farko: Burkina Faso da Gabon (Limbe Stadium, Limbe)
  • Wasa na biyu: Nigeria da Tunisia (Roumde Adjia Stadium, Garoua)

Litinin 24 ga watan Janairu

  • Wasa na uku: Guinea da Gambia (Kouekong Stadium, Bafoussam)
  • Wasu na hudu: Cameroon da Comoros (Olembe Stadium, Yaounde)

Talata 25 ga watan Janairu

  • Wasa na biyar: Senegal da Cape Verd (Kouekong Stadium, Bafoussam)
  • Wasa na shida: Morocco da Malawi (Stade Ahmadou Ahidjo, Yaounde)

Laraba 26 ga watan Janairu

  • Wasa na bakwai: Ivory Coast da Egypt (Japoma Stadium, Douala)
  • Wasa na takwas: Mali da Equatorial Guinea (Limbe Stadium, Limbe)