Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Hotunan yadda Super Eagles ta casa Sudan
An wallafa
Najeriya ta barje gumi da Sudan a yau Asabar a wasan rukunin na biyu a gasar cin kofin Afirka da ake gudanarwa a Kamaru.
An yi wasan ne a Garoua filin wasa na Roumde Adjia inda rukuni na hudu da ya kunshi Najeriya da Masar da Sudan da kuma Guinea Bissau suke ta su fafatawar.