Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Pierre-Emerick Aubameyang zai koma Arsenal
Gabon ta bai wa Pierre-Emerick Aubameyang izinin komawa Arsenal daga gasar kofin Afirka a Kamaru, domin a duba koshin lafiyarsa.
Mai shekara 32 bai yi wa Gabon wasan da ta yi canjaras da Ghana ba ranar Juma'a, sakamakon kamuwa da cutar korona.
Aubameyang ya kamu da annobad da saukarsa a Kamaru ranar 6 ga watan Janairu.
Zai je ne likitoci su duba koshin lafiyarsa da zarar ya isa Arsenal.
Haka kuma Gabon ta umarci dan wasanta da ke taka leda a Nice, Mario Lemina ya koma gida, sakamakon rashin loshin lafiya.
Aubameyang wanda ya kamu da annobar a cikin watan Agusta, bai buga wa Gunners tamaula ba, tun bayan da ta karbe mukamin kyaftin daga wajensa kan halin rashin da'a da ya yi.
Gabon ta sanar da cewar an kara samun wasu 'yan wasanta dauke da cutar korona ranar Litinin.
'Yan kwallon sun hada da Denis Bouanga da Noubi Fotso da David Sambissa da Serge Ngouali da kuma Ulrick Eneme Ella da ba za su buga mata karawa da Morocco ranar Talata ba.