Ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afrika ta Kudu sun isa Legas
Jirgin farko na ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afrika ta Kudu sun isa gida da safiyar yau Alhamis.
Mutanen da aka kwashe su kusan 270 sun sauka ne a filin jirgin saman ƙasar da ke jihar Legas.
Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya yi jigilar mutanen, yayin da gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen kwashe su.
Ƙasashen Afrika da dama sun kwashe mutanensu daga Afrika ta Kudu saboda hare-haren ƙyamar baƙi da ke faruwa a ƙasar.
Ghana da Mozambique sun riga sun kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarsu.
Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana nazarin matakin da za ta ɗauka domin maida martani game da abin da ke faruwa.
Hukumomi sun ce zuwa yanzu an tantance sama da ƴan Najeriya 500 da za su koma gida, kuma ana ci gaba da tantancewar.