Anthony Martial ya ce Ralf Rangnick ya yi masa kazafi cewar bai yadda ya buga wasan Aston Villa ba

An wallafa

Anthony Martial ya yi watsi da kalaman kocin rikon kwaryan Manchester United, Ralf Rangnick da ya ce dan kwallon Faransa bai yadda ya buga karawa da Aston Villa ba.

United ta tashi 2-2 a gasar Premier League da Aston Villa a Villa Park ranar Asabar, inda take cin kwallo ana farkewa.

Tun a baya Martial ya nemi izini a wajen Rangnick cewar yana son barin United a wannan watan, kuma Sevilla ce ke so daukar dan kwallon.

''Ba zan taba kin buga wa Man United wasa ba,'' kamar yadda dan wasan mai shekarar 26 ya sanar a kafar sada zumuntarsa.

''Ina kungiyar nan shekara bakwai ban taba rashin kirki ba, kuma ba zan taba kin martaba United da magoya bayanta ba.''

Sevilla ta kasa cimma kunshin kwantiragi da kudin da United ta gindaya kan daukar aron dan kwallon tawagar Faransa a Janairun nan.

Martial ba a fara wasan Premier League da shi ba tun 2 ga watan Oktoba, bai yi wa kungiyar wasa ba, tun bayan 3-2 da Arsenal ranar 2 ga watan Disamba.

Yanzu da kungiyar ke fama da 'yan wasa da ke jinya da wadanda suka je Afcon da wadanda suka killace kansu, sakamakon cutar korona, Rangnick ya tambayi Martial ko yana son ya buga wasan Aston Villa shi kuma ya ce baya sha'awa.

''Baya son ya buga mana wasa kawai,'' in ji Rangnick.

''Ya kamata ya koma taka leda kamar yadda ya saba, amma baya son hakan, kuma shine dalilin da bai je karawa da Aston Villa ba.''

Martial ya ci kwallo 56 a wasa 173 da ya yi wa United a Premier League.

Cikin watan Janairun 2019 a karkashin Ole Gunnar Solskjaer, Martial ya tsawaita yarjejeniyarsa a United da za ta kare a karshen kakar 2024.