Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Anthony Martial ya nemi izinin barin Manchester United
Anthony Martial ya nemi izinin barin Manchester United daga wajen kocin rikon kwarya, Ralf Rangnick.
Rangnick ya ce ya dauki lokaci mai tsawo yana tattaunawa da dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 26, wadda ya shaida masa cewar yana son gwada sa'a a wata kungiyar.
Wasa biyu Martial ya buga a kakar bana a Premier League da cin kwallo daya.
Duk da cewar dan wasan na son barin Old Trafford a bana, Rangnick ya ce kawo yanzu ba wata kungiyar da ta taya dan kwallon.
Wakilin dan wasan, Philippe Lamboley ya fada tun a farkon watan nan cewar Martial na son barin United a Janairu, zai kuma mika bukatar hakan ga kungiyar nan gaba.
Rangnick ya ce dan wasan ya sanar da shi cewar ya yi shekara bakwai a Old Trafford, lokaci ya yi da ya kamata ya fuskanci wani kalubalen a wata kungiyar.
Martial ya koma United da taka leda a 2015 daga Monaco kan fam miliyan 36 a matakin matashi mafi tsada da aka saya a duniya a lokacin.
Ya ci kwallo 79 a wasa 268 da ya yi wa United, sai dai baya samun buga wasannin sosai tun bayan da kungiyar ta sayo Cristiano Ronaldo da Edinson Cavani da kuma Jadon Sancho.
Dan kwallon tawagar Faransa bai buga wasa ko daya ba karkashin Rangnick, kuma karawa 10 ya yi wa United a dukkan fafatawa a bana.