Kungiyoyin Premier sun fi kashe kudi a cefanen 'yan wasa a 2021

An wallafa

Kungiyoyin gasar Premier ta Ingila sun kashe sama da fam biliyan daya wurin cefanen 'yan wasa a 2021 kamar yadda wani rahoton Fifa ya bayyana.

Bakwai daga cikin ciniki 10 mafi tsada, ya shafi ƴan wasan da aka sayo zuwa Ingila, Chelsea da ta karbo Rumelu Lukaku kan fam miliyan 97.5 shi ne ciniki mafi tsada.

Sayen Jadon Sancho kan fam miliyan 73 da Manchester United ya sa ta zama ƙungiyar da ta fi kashe kudi, inda ta sha gaban Chelsea.

Daga cikin kungiyoyin 20 na Turai da suka fi kashe kuɗi a 2021, 10 daga cikinsu daga Ingila ne.

Manchester City ita ce ta takwas a jerin ƙungiyoyin, ko da yake ba a lissafa da ɗan wasan Aston Villa ba da City ta saya Jack Grealish kan fam miliyan 100 saboda cinikin gida ne.

A jimlace ƙungiyoyin Ingila sun kashe fam biliyan 1.01 a cefanen ƴan wasa daga waje. Italiya ce ta biyu inda ƙungiyoyi suka kashe fam miliyan 486.

Jimillar kuɗin da aka kashe a 2021 sun kai fam biliyan 3.54, inda aka samu raguwa da kashi 13.6 idan aka kwatanta da 2020.

A karon farko kuma rahoton ya ce an fi kashe kuɗi kan ƴan wasan Faransa fiye da sauran ƴan wasan a wasu ƙasashe.

Yan wasan Ingila da suka fi kashe kudi a 2021

1. Manchester United

2. Chelsea

3. RB Leipzig

4. Roma

5. Arsenal

6. Tottenham

7. PSG

8. Manchester City

9. Bayer Leverkusen

10. AC Milan

11. Marseille

12. Juventus

13. Atletico Madrid

14. Norwich

15. Brighton

16. Villarreal

17. Monaco

18. Aston Villa

19. Leicester20. Liverpool

Yan wasa 10 mafi tsada

1. Romelu Lukaku (Inter - Chelsea)

2. Jadon Sancho (Borussia Dortmund - Manchester United)

3. Achraf Hakimi (Inter - PSG)

4. Raphael Varane (Real Madrid - Manchester United)

5. Tammy Abraham (Chelsea - Roma)

6. Ibrahima Konate (RB Leipzig - Liverpool)

7. Martin Odegaard (Real Madrid - Arsenal)

8. Amad Diallo (Atalanta - Manchester United)

9. Eduardo Camavinga (Rennes - Real Madrid)

10. Bryan Gil (Sevilla - Tottenham)