Afcon 2021: Manyan 'yan kwallon da za su ja hankali a Kamaru

An wallafa

Gasar cin kofin Afirka kamar bajekoli ce ta ƴan wasa a nahiyar, kuma tana ɗaya daga cikin gasar da manyan zaratan ƴan ƙwallon duniya ke haɗuwa a wuri ɗaya.

Gasar karo na 33 da za a soma a Kamaru a ranar Lahadi ta ƙunshi fitattun ƴan wasa da kuma masu tasowa da za su nuna bajintarsu.

Gasar ta ƙunshi ƴan wasa dama da ke taka leda a manyan gasa na Turai da ƙasashen Larabawa da kuma matasa da ke murza leda a cikin gida Afirka.

Kusan ƴan wasa 40 daga gasar Premier ta Ingila ake sa ran za su haska a gasar.

Mohamed Salah

Salah na cikin zaratan ƴan ƙwallon duniya da idon duniya zai mayar da hankali akansa.

Dan wasan na Masar yana kan ganiyarsa musamman a ƙungiyar Liverpool da yake taka leda.

Zuwa yanzu shi ne wanda ya fi yawan cin ƙwallaye a gasar Premier ta Ingila.

Salah na cikin tawagar Masar da zai haska a Kamaru.

Riyad Mahrez

Mahrez na cikin manyan zaratan ƴan ƙwallon Afrika wanda ke taka leda a Manchester City Ɗan wasan shi ne kaftin din tawagar Algeria, kuma babban ƙalubalensa shi ne jagorantar ƙasar ga nasarar ɗaukar kofin Afrika karo na biyu a jere, bayan lashe kofin a 2019.

Mahrez ya kasance ɗan wasa mai matuƙar muhimmanci ga Guardiola a Manchester City, haka ma a tawagar Algeria.

Yana cikin masu ci wa City ƙwallaye inda a bana zuwa yanzu ya jefa ƙwallo shida a raga kuma ya taimaka sau huɗu aka ciki.

Mahrez na cikin ƴan ƙwallon da za su ja hankalin duniya a gasar cin kofin Afirka a Kamaru, kamar yadda ya ja hankali a 2019 musamman wasan dab da ƙarshe da ya Algeria ta fitar da Najeriya

Sadio Mane

Sadio Mane ne ke tashe a tawagar Senegal, kuma ɗaya daga cikin ƴan wasan da Liverpool ke dogaro da su wajen cin ƙwallaye da taimakawa a ci.

Mane yana cikin zaratan ƴan ƙwallon Afirka da ke wasa a Turai da duniya za ta sa wa ido a gasar cin kofin Afirka.

Ƙalubalen da ke gaban Mane shi ne jagorantar Senegal ga nasarar lashe kofin Afirka a Kamaru.

Zuwa yanzu Mane ya ci wa Liverpool ƙwallo 10 a wasannin da ya buga a kakar bana.

Pierre-Emerick Aubameyang

Pierre-Emerick Aubameyang kaftin ɗin Gabon da ke taka leda a Arsenal na cikin zaratan ƴan ƙwallon Afirka da za su haska a Kamaru.

Ko da yake ɗan wasan ya kamu da korona kafin soma gasar wanda ya sa ya killace kansa har sai lokacin da gwaji ya tabbatar da ba ya dauke da cutar.

Aubameyang shi ya fi yawan cin ƙwallaye a Gabon, kuma ya taba lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika.

Dan wasan wanda aka haifa a Faransa ya fara takawa Gabon Kwallo ne a 2009, kuma ya wakilci Gabon a gasar cin kofin Afirka sau huɗu.

Edouard Mendy

Ana ganin Édouard Mendy na Chelsea a matsayin golan da babu kamarsa a gasar cin kofin Afirka.

Mendy yana cikin gola guda uku da ke takarar lashe kyautar gwarzon gola ta FIFA ta bana.

Kamar yadda ake ganin ya taimakawa Chelsea lashe kofin zakarun Turai, Mendy zai yi tasiri sosai ga Senegal da za ta yi fatan huce hushin rashin nasara a hannun Algeria a wasan ƙarshe a 2019.

Franck Kessie

Ivory Coast na ɗaya daga cikin manyan ƙasashen da ake ganin za su lashe gasar cin kofin Afirka a Kamaru, musamman zaratan ƴan ƙwallo da ta ƙunsa irinsu Franck Kessie ɗan wasan tsakiya.

Kessie da ke taka leda a AC Milan yana kan ganiyarsa, inda ya ci ƙwallo biyar a kakar bana a Seria A.

Yana cikin manyan ƴan wasan da za su ja hankali a Kamaru. deep.

Achraf Hakimi

Ɗan wasan Morocco da Paris Saint-Germain, Hakimi yana cikin matasan ƴan wasan da za su ja hankali a gasar cin kofin Afirka a Kamaru

Hakimi ɗan wasan baya yana tasiri a tawagar Morocco, musamman kawo ƙwallo a ci.

Umar Sadiq

Umar Sadiq matashi ne da ke lokaci a kulub dinsa Almeria.

Dan wasan na Najeriya mai shekara 24, zai ja hankali musamman iya yanke da yin barazana ga ƴan wasan baya.

Ɗan wasan yana taka rawa sosai a Almeria da harin tsallakowa zuwa gasar La liga a Spain.