Mourinho ya yabi kokarin Anthony Martial

An wallafa

Kocin Manchester United, Jose Mourinho ya yaba wa Anthony Martial a kan ci gaban da yake ba wa kungiyar a kakar bana.

Martial ya ci kwallo a baya-bayan nan a duk wasa uku da United ta buga a gasar Premier har da wadda ya ci Burnley inda kungiyarsa ta hada maki uku a ranar Asabar.

Dan wasan na kasar Faransa, mai shekara 22 ya ci kwallo 11 a bana, bayan a bara baki daya ya ci kwallo takwas.

Mourinho ya ce kokarin dan wasan ya karu tun a bara, musamman yadda yake buga wasan gefe daga gaba, inda yake karawa United kwarin gwiwa.

Martial ya koma United a shekarar 2015 daga Monaco wadda ya yi wa wasa 49 ya kuma ci kwallo 11.